Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Da Amincewarmu Amurka Ta Ƙaddamar Da Hari – Gwamnatin Nijeriya

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta ce sai da ta amince tare da bayar da izini kafin gwamnatin Amurka ta ƙaddamar da harin bam a ƙasar. Ministan ...



Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta ce sai da ta amince tare da bayar da izini kafin gwamnatin Amurka ta ƙaddamar da harin bam a ƙasar.

Ministan Harkokin Wajen Nijeriya, Yusuf Tuggar ne ya bayyana haka a zantawarsa da tashar Channels, inda ya ce Shugaba Bola Tinubu yana sane da harin kafin a ƙaddamar.

Shugaban Amurka Donald Trump ne ya sanar da ƙaddamar da hari a jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin Nijeriya, lamarin da ya ɗaga hankalin ’yan ƙasar.

Da yake jawabi kan harin a safiyar Juma’a, Tuggar ya ce, “yanzu da Amurka ta fara ba mu haɗin kai, za mu ci gaba da aikin ne a tare, kuma kamar yadda shugaban ƙasa ya nanata a jiya kafin ya amince da harin, dole aikin ya zama aikin haɗin gwiwa, kuma dole ya zama babu wani addini da ake hari,” inji shi.

Ya ce Nijeriya ƙasa ce mai addinai da dama, sannan ya ƙara da cewa gwamnatin Nijeriya ba ta ce amince a mata karan-tsaye a kan ’yancinta ba.

No comments