Fadar Shugaban Ƙasa ta musanta wani labari na ƙarya da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke ikirarin cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sauya...
Fadar Shugaban Ƙasa ta musanta wani labari na ƙarya da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke ikirarin cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sauya Shugaban Ma’aikatan Fadarsa (Chief of Staff), Hon. Femi Gbajabiamila, da Babban Sakataren Sirrinsa (Principal Private Secretary), Hakeem Muri-Okunola.A cikin wata sanarwa da Fadar Shugaban Ƙasa ta fitar a ranar Alhamis, ta bayyana cewa babu wata gaskiya ko kaɗan a cikin wannan ikirari, tare da kira ga ’yan Najeriya da su yi watsi da labarin gaba ɗaya.
Sanarwar ta jaddada cewa Hon. Femi Gbajabiamila na nan daram a matsayin Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, yayin da Hakeem Muri-Okunola shi ma ke ci gaba da gudanar da aikinsa a matsayin Babban Sakataren Sirri. Ta ce babu wani sauyi da aka yi a wadannan mukamai.
Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana cewa labarin da ke yawo ƙirƙirarre ne daga wasu masu yaɗa labaran ƙarya da nufinsu shi ne tayar da zaune tsaye da rashin jituwa a cikin gwamnati.
Haka kuma, ta sake jan hankalin kafafen yaɗa labarai da masu amfani da kafafen sada zumunta da su rika tantance sahihancin duk wani bayani kafin wallafawa ko yadawa.
Sanarwar ta samu sa hannun Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Harkokin Yaɗa Labarai da Tsare-tsare, Bayo Onanuga, a ranar 25 ga Disamba, 2025.
No comments