Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Nijeriya Da Amurka Sun Kai Harin Haɗin Gwiwa Kan Manyan Maboyar ’Yan Ta’adda A Arewa Maso Yamma

Ma’aikatar Harkokin Waje ta Nijeriya ta tabbatar da cewa gwamnati na ci gaba da haɗin gwiwar tsaro da ƙasashen duniya, musamman Amurka domin...


Ma’aikatar Harkokin Waje ta Nijeriya ta tabbatar da cewa gwamnati na ci gaba da haɗin gwiwar tsaro da ƙasashen duniya, musamman Amurka domin daƙile barazanar ta’addanci a ƙasar. Wannan mataki, a cewar ma’aikatar, ya haifar da samun ƙarin nasarori a yunƙurin kai hare-haren jiragen sama da suka yi a wasu sansanonin ’yan ta’adda a yankin Arewa maso Yamma.

A wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar ɗauke da sa hannun Mataimakin Kakakin Ma’aikatar, Kimiebi Imomotimi Ebienfa, an bayyana cewa haɗin gwiwar tsaron ya ƙunshi musayar bayanan sirri, dabarun tsaro, da sauran nau’ikan goyon baya da suka dace da ka’idojin ƙasa da ƙasa tare da mutunta ikon kowace ƙasa.

Sanarwar ta ce, duk wani yaki da ta’addanci a Nijeriya na gudana ne da nufin kare rayukan fararen hula, tabbatar da haɗin kan ƙasa da kuma kiyaye mutuncin kowane ɗan ƙasa ba tare da la’akari da addini ko ƙabila ba. 

Gwamnatin Tarayya na ci gaba da amfani da hanyoyin diflomasiyya da tsaro tare da abokan hulda domin tarwatsa gungun ’yan ta’adda, katse hanyoyin samun kudadensu da kuma hana su samun sabbin maboya, tare da karfafa cibiyoyin tsaron gida da kayan leken asiri.

Ma’aikatar ta bayyana cewa za ta ci gaba da wayar da kan jama’a da sanar da al’umma duk wani ci gaba da aka samu a yaki da ta’addanci ta hanyar shafuka da tashoshin gwamnati da suka dace.

Sanarwar ta fito daga Ma’aikatar Harkokin Waje, Abuja, ranar Juma’a 26 ga Disamba, 2025.
 

No comments