Shugaba Bola Ahmad Tinubu, ya taya tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, kuma abokin siyasarsa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, murnar zagayowa...
Shugaba Bola Ahmad Tinubu, ya taya tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, kuma abokin siyasarsa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, murnar zagayowar ranar haihuwarsa da yake yi yau Alhamis, 25 ga Disamba, yana cika shekaru 76 da haihuwa.A cikin wata sanarwa da mai ba Shugaban ƙasa shawara kan harkokin bayanai da dabaru, Bayo Onanuga ya fitar, Shugaba Tinubu ya bayyana Dr. Ganduje a matsayin gogaggen ɗan siyasa kuma ƙwararren mai gudanar da mulki, wanda ya shafe kusan rabin ƙarni yana bai wa ƙasa hidima a fannoni da dama.
Shugaban ya bayyana cewa, Dr. Ganduje ya fara taka rawa tun a gwamnatin tarayya, inda ya yi aiki a matsayin babban jami’in gudanarwa a Babban Birnin Tarayya Abuja, kafin daga bisani a kira shi Kano domin ya zama Kwamishinan Ayyuka a lokacin mulkin soja.
Kazalika, ya tuna cewa Ganduje ya yi mataimakin gwamnan Kano na tsawon wa’adi biyu, sannan daga bisani ya zama gwamnan jihar, inda ya yi shekaru takwas yana jagorancin Kano. Yanzu haka kuma, yana riƙe da kujerar Shugaban Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama ta ƙasa (FAAN).
“Ina alfahari da zumunci da haɗin kai tsakaninmu tun tsawon shekaru, da irin gudummawar da ya bayar ga jam’iyyar APC. Ina roƙon Allah Ya ƙara masa lafiya da nisan rai domin ci gaba da hidima ga Najeriya da bil’adama,” in ji Shugaba Tinubu.
Sanarwar ta ƙare da taya shi murna tare da fatan alheri a cikin sabuwar shekarar rayuwar da ya samu.
No comments