Daga Ibrahim Muhammad, Kano An tabbatar da rasuwar ’yan Majalisun Dokokin Jihar Kano guda biyu, Hon. Aminu Sa’adu Ungoggo, mai wakiltar Ƙara...
Daga Ibrahim Muhammad, Kano
An tabbatar da rasuwar ’yan Majalisun Dokokin Jihar Kano guda biyu, Hon. Aminu Sa’adu Ungoggo, mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Ungoggo da kuma Hon. Sarki Aliyu Daneji mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Birnin Kano, wanda wannan rashi ya jefa majalisar cikin jimami da kaɗuwa.
Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano, Malam Kamaludeen Sani Shawai ne ya tabbatar da rasuwar Hon. Aminu Sa’adu Ungoggo a yammacin yau Talata yayin da yake zantawa da manema labarai.
A cewar sa, marigayin Ɗan Majalisar mai wakiktar Ungogo, Hon Aminu Sa'adu ya kamu da rashin lafiya ne jim kaɗan bayan ya isa Majalisar a safiyar ranar Laraba nan take aka garzaya da shi zuwa asibiti domin samun kulawar likitoci.
Daga bisani aka tabbatar da rasuwar sa.
Shi kuma ɗan Majalisar Jiha mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Birnin, Hon. Sarki Aliyu Daneji ya rasu ne jim kaɗan da jin rasuwar ɗan majalisar Ungoggo, kamar yadda mai magana da Gwamnan Jihar Kano, Hon Sunusi Bature Dawakin Tofa ya sanar.
Tuni dai an gudanar da jana'izar Ɗan Majalisar jiha na Ungogo, Hon. Aminu Sa'ad, yayin da shi kuma Ɗan Majalisar Birnin Kano, Hon. Sarki Aliyu za a yi masa jana'iza a safiyar Alhamis.

No comments