’Yan Nijeriya a faɗin ƙasar nan sun gudanar da hadahadar kuɗaɗe cikin sauƙi a lokacin Kirsimeti na 2025. Har zuwa ranar 28 ga Disamba, bab...
’Yan Nijeriya a faɗin ƙasar nan sun gudanar da hadahadar kuɗaɗe cikin sauƙi a lokacin Kirsimeti na 2025. Har zuwa ranar 28 ga Disamba, babu rahotannin samun cikas ko ƙarancin kuɗi a ATM da bankuna a faɗin ƙasar nan.
Yayin da matsalar ƙarancin kuɗi ta addabi bukukuwan Kirsimeti na bara, a bana ta ragu sosai, lamarin da ya kawo sauƙi ga iyalai, ’yan kasuwa da kamfanoni.
A irin wannan lokaci a bara, ƙarancin yawo da kuɗi da wahalar cire kuɗi daga bankuna da na’urorin ATM sun jefa mutane cikin ƙalubale mai tsanani. ’Yan Nijeriya da dama sun sha wahalar tsayawa dogayen layuka a bankuna, fuskantar gazawar cire kuɗi daga ATM akai-akai sai kuma ƙuntatawar samun kuɗi, wanda ya kawo cikas ga harkokin kasuwanci tare da rage armashin bukukuwan Kirsimeti.
Sai dai a wannan shekara, binciken da wakilin mu ya gudanar ya nuna cewa lokacin Kirsimeti ya kasance cikin sauƙi, inda bankuna da ATM ke aiki yadda ya kamata, tare da ƙarancin koke-koken jama’a.
An gano cewa a manyan birane da ƙauyuka ma, ’yan Nijeriya sun samu sauƙin cire kuɗi, wanda ya ba su damar biyan buƙatun Kirsimeti ba tare da irin damuwar da suka fuskanta a bara ba.
A cewar masana harkar kuɗi, wannan ci gaba ya samo asali ne daga tsauraran gyare-gyaren da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya aiwatar domin magance tushen matsalar ƙarancin kuɗin da aka fuskanta a baya.
An kuma gano cewa babban bankin ya ɗauki mataki kai tsaye ta hanyar ƙaddamar da matakai da nufin inganta yawo da kuɗi da kuma ƙarfafa tsarin sarrafa kuɗi a dukkan bankuna.
Wakilin mu ya ji cewa muhimmin ɓangare na wannan haɓɓasa da CBN ya yi, shi ne kafa wani kwamitin da Gwamnan Babban Bankin Nijeriya, Olayemi Cardoso ke jagoranta.
An ba kwamitin, bisa ga binciken da aka yi, alhakin duba matsalolin da ke shafar samuwar kuɗi a Nijeriya gaba ɗaya.
Har ila yau, binciken ya nuna cewa kwamitin ya duba dukkan sarƙaƙiyar samar da kuɗi, tun daga bugawa da rarraba kuɗi, zuwa ayyukan bankuna da cika ATM da kuɗi.
’Yan kasuwa, waɗanda su ne suka fi shan wahala a lokacin ƙarancin kuɗi na bara, sun shaida wa wakilin mu cewa bambancin da ke akwai a wannan Kirsimeti ya yi yawa sosai.
Wani ɗan kasuwar kayan abinci, John Uzor, ya ce yawan yawo da kuɗi ya fi na bara nesa ba kusa ba, wanda ya ba shi damar gudanar da kasuwanci ba tare da cikas ba. “Bara a lokacin Kirsimeti, kwastomomi suna so su saya amma ba su samun kuɗi, kuma tura kuɗi ta banki na yawan ƙin tafiya ko an tura kuɗin. Wannan shekarar kuwa, mutane na zuwa da kuɗi, kuma kasuwanci ya inganta,” inji shi.
Haka kuma, wani mai POS a Abuja mai suna Ibrahim Usman ya ce samuwar kuɗi a ATM ta rage matsin lamba ga masu POS.
“A bara, mutane sun dogara da mu sosai, kuma kuɗi yana da wuya a samu. Yanzu ATM na bada kuɗi, kuma tashin hankali ya ragu,” inji shi.
Sauran ’yan Nijeriya sun bayyana irin wannan ra’ayi. Wata ma’aikaciyar gwamnati a Abuja, Blessing George, ta ce rashin dogayen layuka a ATM ya sa shirye-shiryen bukukuwan sun fi sauƙi.
“Ina iya cire kuɗi duk lokacin da nake buƙata. Babban sauƙi ne idan aka kwatanta da abin da muka fuskanta a bara,” cewar ta.
Ƙananan ’yan kasuwa ma sun yaba da wannan ci gaba, suna cewa ingantaccen tsarin yawo da kuɗi ya ƙara ƙwarin gwiwar masu saye da yawan kashe kuɗi.
Mutane da dama da suka tattauna da wakilin mu sun ce waɗannan gyare-gyaren sun taimaka wajen daidaita mu’amalar yau da kullum, musamman ga ’yan Nijeriya da har yanzu ke dogaro sosai da riƙe kuɗi a hannu idan za su ya hadahada, gudun kada su samu matsalar kasa tura kuɗi daga asusun bankin su zuwa wani asusun banki.
No comments