Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Babban Bankin Nijeriya Ya Yi Gargaɗin A Guji Wulaƙanta Naira A Lokacin Shagulgulan Ƙarshen Shekara

Babban bankin Nijeriya CBN yana ci gaba da gargaɗi, tare da jawo hankalin al'umma da su guji wulaƙanta takardun Naira, musamman a lokaci...


Babban bankin Nijeriya CBN yana ci gaba da gargaɗi, tare da jawo hankalin al'umma da su guji wulaƙanta takardun Naira, musamman a lokacin bukukuwa.

A wata takarda da ta fito daga ofishin hulɗa da jama'a da yaɗa labarai, Babban bankin ya jawo hankalin al'umma cewa a tuna fa, darajar Naira, darajar ƙasar mu ce.

Wasu halayen da Babban bankin ya kawo matsayin wulaƙanta Naira, sun haɗa da kekketa Naira, duƙunƙune Naira, buga kuɗaɗe na jabu, shafa wa Naira datti da lilliƙawa a wuraren bukukuwa. 

No comments