Darakta Janar na Hukumar Kula da Al’amuran Filaye na Jihar Kaduna (KADGIS), Dokta Bashir Garba Ibrahim, ya bayyana cewa bayar da takardun ma...
Darakta Janar na Hukumar Kula da Al’amuran Filaye na Jihar Kaduna (KADGIS), Dokta Bashir Garba Ibrahim, ya bayyana cewa bayar da takardun mallakar filaye ga masu buƙata ta musamman a jihar ya biyo bayan umarnin da Mai Girma Gwamnan Jihar Kaduna, Kwamared Sanata Uba Sani ne ya bayar.Dokta Bashir Garba Ibrahim ya bayyana hakan ne yayin da ya ke ganawa da manema labarai a ofishin sa da ke Kaduna, a lokacin da ya miƙa takardun mallakar filayen ga wasu daga cikin masu buƙata ta musamman.
Ya ce, Gwamna Uba Sani ya bayar da umarnin ne domin a saka wa masu buƙata ta musamman bisa irin gudumawar da suka bayar a lokacin yaƙin neman zabe da kuma lokacin gudanar da zaben da ya kai shi ga nasarar zama Gwamnan Jihar Kaduna.
“A bisa wannan tsari ne aka nemi waɗannan mutane masu buƙata ta musamman. Bayan sun zo, aka sanar da Mai Girma Gwamna, wanda nan take ya bayar da umarni a ba su waɗannan takardun filaye.
"A yau mun kira su tare da miƙa musu saƙon Gwamna ta hanyar ba su takardun mallakar filayen, domin su amfana da irin gudumawar da suka bayar tun lokacin neman zabe,” in ji Dokta Bashir.
Ya ƙara da cewa akwai ƙungiyoyi da dama da Gwamna Uba Sani ya bayar da umarnin a kula da su, kuma hukumar KADGIS na bin umarnin ne a hankali ɗaya bayan ɗaya domin tabbatar da adalci da gaskiya.
Dokta Bashir Garba Ibrahim ya jaddada cewa ba a taba samun gwamnatin da ta riƙa bayar da filaye ga jama’a kamar yadda gwamnatin Sanata Uba Sani ke yi ba.
“Ba kawai waɗanda suka taimaka ba, hatta waɗanda ba su taimaka ba ma ana tallafa musu. Wannan gwamnati ta ƙudiri aniyar taimaka wa al’umma, kuma da yardar Allah za mu ci gaba da aiwatar da umarnin Gwamna domin jin daɗin jama’a,” in ji shi.
Ya bayyana cewa adadin waɗanda aka bai wa takardun mallakar filayen a wannan karo sun kai mutane talatin (30), daga sassa daban-daban na jihar, kuma dukkan su na cikin masu buƙata ta musamman.
Da yake tofa albarkacin bakin sa bayan karbar takardun, Salisu Isa, mazaunin Ƙaramar Hukumar Kaduna ta Arewa, kuma Mataimakin Shugaban Ƙungiyar Masu Buƙata Ta Musamman ta Kaduna ta Tsakiya (Kaduna Central Disable Development Association), ya bayyana farin cikin su, tare da nuna godiya ga Gwamna Uba Sani da Daraktan Janar na KADGIS.
Salisu Isa ya ce ƙungiyar su na goyon bayan Gwamna Uba Sani ɗari bisa ɗari, ba wai ɗari bisa ɗari kaɗai ba, har dubu bisa dubu.
“Duk inda Gwamna Uba Sani yake, muna kai kai mu gan shi ne saboda ba mu taba samun Gwamna da ya daraja nakasassu kamar shi ba. Ya ba mu aiki, ya ba mu abin yi, ya kuma ba mu mutunci,” in ji Salisu.
Ya ƙara da cewa tun da suke ‘yan asalin Jihar Kaduna, ba su taba samun wurin zama da za su ce mallakarsu ba, sai a wannan gwamnatin ta Uba Sani.
“A wannan karon, Gwamna ya umarci a taimake mu ɗari bisa ɗari. An ba mu filaye, an ce mu je mu gina mu zauna da iyalan mu. Kuma da ikon Allah, babu ko ɗaya a cikin ƙungiyar mu da zai sayar da filin sa; kowa gini zai yi ya zauna,” in ji shi.
Salisu Isa ya kuma miƙa godiya ta musamman ga Daraktan Janar na KADGIS, Dokta Bashir Garba Ibrahim, bisa kokarin da ya yi na kai koken Ƙungiyar su zuwa ga Mai Girma Gwamna, lamarin da ya kai ga samun wannan ta@llafi.
“Muna godiya mara misaltuwa, domin mun daɗe muna neman irin wannan taimako amma ba a taba yi mana ba, sai a wannan lokaci,” in ji shi.
No comments