Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana matuƙar kaɗuwa da alhini kan rasuwar wasu ‘yan jarida bakwai a wani...
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana matuƙar kaɗuwa da alhini kan rasuwar wasu ‘yan jarida bakwai a wani mummunan haɗarin mota guda ɗaya da ya faru a yankin Gombe ta Kudu, Jihar Gombe, a ranar Litinin.
Lamarin ya faru ne da yammacin Litinin yayin da ‘yan jaridar suke dawowa daga bikin aure a Mazaɓar Sanatan Gombe ta Kudu.
Rahotanni sun nuna cewa sun yi tafiyar ne domin halartar bikin auren wani abokin aikin su daga Hukumar Talbijin ta Nijeriya (NTA).
A cewar bayanan farko daga Kwamandan Sashen Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Tarayya (FRSC) a Jihar Gombe, Samson Kaura, haɗarin ya kasance mai muni kuma ya yi sanadin mutuwar mutanen.
Ministan ya bayyana wannan ibtila'i a matsayin babban rashi mai ratsa zuciya ga al’ummar kafafen yaɗa labarai da kuma ƙasa baki ɗaya, inda ya ce ‘yan jaridar sun kasance muryoyi masu jajircewa da ke wayar da kan jama’a cikin jarumtaka, gaskiya da ƙwarewa.
Ya ce: “Wannan lokaci ne mai raɗaɗi ƙwarai. Nijeriya ta rasa muryoyi masu sadaukarwa da suka riƙa sanarwa, ilimantarwa da tsayawa kan gaskiya. Rashin su babban koma-baya ne gare mu duka.”
Idris ya miƙa ta’aziyyar sa ga Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Nijeriya (NUJ), Majalisar 'Yan Jarida ta Jihar Gombe, da kuma musamman iyalai, abokai da abokan aikin mamatan.
Ya yi addu’ar Allah ya ba su ƙarfin jure wannan babban rashi, yana cewa, “Tunanin mu da addu’o’in mu suna tare da iyalan su da masoyan su.
"Allah Maɗaukakin Sarki ya ba su haƙuri, ya kuma jiƙan su da rahama, ya sa sun huta.
“Mun tsaya tsayin daka tare da NUJ da dukkan al’ummar kafafen yaɗa labarai a wannan lokaci mai wahala. Dole ne mu ci gaba da aiki tare domin inganta matakan tsaro ga waɗanda ke hidimta wa ƙasa a kullum,” in ji shi.
Ya tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya na tare da iyalan da abin ya shafa da kuma al’ummar kafafen yaɗa labarai a wannan lokaci na jimami.

No comments