Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga Gwamnati da al’ummar Jihar Kano bisa rasuwar ’yan Majalisar Dokokin jiha...
Marigayan su ne Aminu Sa’ad Ungogo da Aliyu Sarki Daneji, wakilan mazabun Ungogo da Kano Municipal, waɗanda suka rasu a lokuta daban-daban cikin awa ɗaya a ranar Laraba.
Shugaba Tinubu ya bayyana rasuwar tasu a matsayin abin bakin ciki, mai raɗaɗi da girgiza zukata, yana mai cewa mutuwar ta bar giɓi mai girma tare da hana al’ummar mazabunsu wakilci na kwazo da jajircewa.
Shugaban ya ce:
“Na miƙa ta’aziyyata ga iyalansu da al’ummar mazabunsu, tare da Gwamnati da jama’ar Jihar Kano.
“Haka kuma ina jajanta wa Shugabanni da dukkan ’yan Majalisar Dokokin Jihar Kano kan rasuwar abokan aikinsu”
Shugaban Ƙasa ya yi addu’ar Allah Ya jikan marigayan, Ya kuma bai wa iyalansu da dukkan waɗanda abin ya shafa haƙuri.
No comments