Rahotanni Jihar Borno na cewa an ji ƙarar abin fashewa a wani masallaci a birnin Maiduguri, wanda zuwa yanzu ya yi ajalin aƙalla mutum 7, sa...
Rahotanni Jihar Borno na cewa an ji ƙarar abin fashewa a wani masallaci a birnin Maiduguri, wanda zuwa yanzu ya yi ajalin aƙalla mutum 7, sannan wasu da dama suka jikkata.
Kawo yanzu babu wata ƙungiya da ta ɗauki alhakin kai wannan harin, wanda ake kyautata zaton na ƙunar baƙin wake ne.
Wani ganau ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa sun fara da jin ƙara mai ƙarfin gaske, daga nan kuma sai baƙin hayaƙi ya turnuƙe masallacin da ke kasuwar Gamborou a jihar.
Harin ya faru ne lokacin sallar Magariba.
Jihar Borno da kewaye na fama da hare-haren masu tada ƙayar baya na Boko Haram, inda suke kai hare-hare a makarantu da wuraren ibada da kasuwanni, duk da yake a 'yan shekarun nan an samu kwanciyar hankali a jihar.

No comments