Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

BAI WA MANYAN MUTANE KARIYA: Sojoji Sun Cafke 'Yan Sanda Huɗu A Abuja

Sojojin Nijeriya sun kama ’yan sanda huɗu da ake zargi suna yin rakiya ga wani babban mutum ba tare da izini ba, lamarin da ya saba wa umarn...


Sojojin Nijeriya sun kama ’yan sanda huɗu da ake zargi suna yin rakiya ga wani babban mutum ba tare da izini ba, lamarin da ya saba wa umarnin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu na janye ’yan sanda daga ayyukan gadin manyan mutane.

Majiyoyin tsaro sun bayyana wa masani kan harkokin tsaro, Zagazola Makama, cewa an kama ’yan sandan ne a ranar 17 ga Disamba da misalin ƙarfe 9:30 na safe, a lokacin da suke kan aikin rakiya.

Waɗanda aka kama sun haɗa da Mataimakin Sufeto na ’Yan Sanda, Musa Waziri, da Sufeto Jeremiah Achimogu, dukkansu daga runduna ta 45 ta 'yan sandan Nijeriya da ke Abuja.

Sauran su ne Sufeto Awipi Terry na 21 PMF da kuma Sufeto Hassan Baba na 50 PMF, Abuja.

A cewar majiyoyin tsaro, dakarun soji ne suka kama su bayan da ake zargin sun karya umarnin shugaban ƙasa da ya haramta wa ’yan sanda yin rakiya ga manyan mutane ba tare da izini na musamman ba.

Rahotanni sun kuma nuna cewa ’yan sandan sun sanya kayan aiki da tufafi masu kama da na Hukumar Tsaro ta NSCDC, lamarin da ake zargin an yi shi ne domin guje wa ganowa da kuma raina hankalin jami’an da ke aiwatar da doka.

Bayan kama su, an tsare ’yan sandan, yayin da hukumomin ’yan sanda suka fara daukar matakan ladabtarwa a kansu bisa tanade-tanaden dokokin rundunar ’yan sanda ta Nijeriya.

No comments