Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Tinubu Na Kafa Ginshiƙai Masu Ƙarfi Don Tsaro, Ci Gaba Da Sabunta Ƙasa – Ministan Yaɗa Labarai

  Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na ɗaukar matakai a tsan...


Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na ɗaukar matakai a tsanake kuma masu muhimmanci domin daidaita tattalin arzikin Nijeriya, ƙarfafa tsaron ƙasa, da kuma shimfiɗa tubalin wadata mai ɗorewa na dogon lokaci.

Ministan ya faɗi hakan ne a daren Juma’a yayin wata liyafar cin abinci tare da ƙungiyoyin goyon bayan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da aka gudanar a Cibiyar Taro ta NAF, Abuja.

Da yake jawabi ga shugabanni da membobin ƙungiyoyin goyon bayan APC, Idris ya gode masu bisa amincin su da ci gaba da goyon bayan da suke bai wa jam’iyyar, inda ya bayyana su a matsayin muhimmin ginshiƙi na jam’iyyar da nasarorin ta. 

Ya ce APC ta karɓi ragamar mulki ne a wani lokaci mai wahala ga ƙasar nan, wanda ya buƙaci yanke manyan shawarwari domin magance tsofaffin matsalolin tattalin arziki da tsaro, tare da sanya makomar Nijeriya a gaba.

A cewar sa, gwamnatin Tinubu ta riga ta fara samun alamu masu kyau daga ajandar gyare-gyaren ta, ciki har da ƙaruwa da amincewar masu zuba jari, ƙarin yawan man da ake haƙowa, ingantaccen samun kuɗaɗen shiga, da kuma bada tallafi na musamman ga jihohi, kasuwanci da ‘yan Nijeriya masu rauni.

Ya jaddada cewa bayyananniyar sadarwa da hulɗa da ‘yan ƙasa na ci gaba da kasancewa ginshiƙai a tsarin aikin gwamnati, yana mai cewa dole ne a yi wa ‘yan Nijeriya cikakken bayani kan gyare-gyare domin gina amincewa da manufa ɗaya ta ƙasa.

Ministan ya kuma yi tsokaci kan ƙimar kasafin kuɗin shekarar 2026 na naira tiriliyan 58.18 da Shugaba Tinubu ya gabatar wa Majalisar Ƙasa a safiyar ranar ta Juma'a, inda ya nuna cewa tsaro da kare ƙasa, ababen more rayuwa, ilimi da kiwon lafiya sun samu fifiko na musamman.

Yayin da yake ambato abin da Shugaban Ƙasa ya faɗa, Idris ya ce waɗannan fannoni huɗu suna da alaƙa ta ƙut-da-ƙut, domin tsaro shi ne ginshiƙin zuba jari, ilimi da lafiya na ƙara yawan aiki da ƙwarewa, yayin da ababen more rayuwa suke tallafa wa samar da ayyukan yi da bunƙasar kasuwanci.

Ya bayyana cewa tsaron ƙasa na ci gaba da kasancewa babban abin da za a ba fifiko a 2026, tare da shirye-shiryen sabunta kayan aikin rundunar sojoji, ƙarfafa aikin ‘yan sanda bisa bayanan sirri, inganta tsaron kan iyakoki, amfani da fasahar zamani wajen sa ido, da kuma tallafa wa samar da zaman lafiya da hana rikice-rikice a matakin al’umma.

Ministan ya bayyana ƙungiyoyin goyon bayan APC a matsayin fiye da masu wayar da kan jama’a a lokacin zaɓe kawai, yana mai cewa su abokan hulɗa ne masu muhimmanci wajen kare gaskiya, yaƙi da yaɗa labaran ƙarya, da kuma bayyana manufofin gwamnati ga jama’a.

Ya buƙace su da su mara wa kasafin kuɗin shekarar 2026 baya, wanda aka yi wa laƙabi da “Kasafin Ƙarfafa Tsari, Sabunta Juriyar Ƙasa da Wadata ta Bai-ɗaya,” tare da taimaka wa ‘yan Nijeriya su fahimci manufofin sa da amfanin sa. 

“A matsayin ku na jakadun jam’iyyar mu, rawar da kuke takawa wajen wayar da kai, sanarwa da ƙarfafa amincewar jama’a da manufofin mu ta fi muhimmanci a yanzu fiye da kowane lokaci,” inji Idris.

Ya tabbatar wa ƙungiyoyin goyon bayan cewa an san sadaukarwar su da gudunmawar su kuma ana yaba masu.

Ya ƙara da cewa gwamnati da jam’iyya na ci gaba da jajircewa kan haɗa kowa, adalci da kuma ba da lada ga aiki tuƙuru.

Ministan ya yi kira da a yi haɗin kai da sabunta ƙudiri kan Ajandar Sabunta Fata, yana mai roƙon ‘yan jam’iyya da su ci gaba da aiki tare da Shugaba Tinubu domin gina Nijeriya mai ƙarfi, mai tsaro, kuma mai wadata.

Taron ya samu halartar Ministan Ƙaramar Hukumar Cigaban Yankuna, Alhaji Uba Maigari; Darakta Janar na Hukumar Talbijin ta Nijeriya (NTA), Abdulhamid Dembos; Darakta Janar na Hukumar Rediyon Tarayya ta Nijeriya (FRCN), Dakta Mohammed Bulama; Darakta Janar na Muryar Nijeriya (VON), Jibrin Baba-Ndace, da kuma shugabannin ƙungiyoyin goyon bayan APC da dama.






 

No comments