Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Sarkin Ɗansadau Ya Naɗa Uwar gidan Gwamnan Zamfara Sarautar 'Yar Gojen Ɗansadau

Daga Hussaini Yero Funtua, Gusau Mai Martaba Sarkin Kudun Ɗansadau, Alhaji Garba Muhammad Sarkin Kudu Atu na II, ya ba Uwargidan Gwamnan Jih...


Daga Hussaini Yero Funtua, Gusau

Mai Martaba Sarkin Kudun Ɗansadau, Alhaji Garba Muhammad Sarkin Kudu Atu na II, ya ba Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal sarauta mai daraja ta 'YAR GOJEN ƊANSADAU, domin yaba wa gudunmawar da ta bayar ga ci gaban zamantakewa, da ƙarfafa mata da kuma ayyukan jin ƙai.

Sakatariyar yaɗa labarai ta Uwargidan gwamnan, Rabi Yusif ce ta bayyana haka a wata sanarwar da ya sa ma hannu ga manaema labarai.

A cewart ta, n ba da wannan sarauta ne a lokacin ziyarar girmamawa da Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya kai a fadar Sarkin da ke Ɗansadau, a Ƙaramar Hukumar Maru.

Sanarwar ta yi bayanin ma''anar "Yar Gojen Ɗansadau, da cewa "Sarauniyar Matan Ɗansadau. Sarkin yana nuna ƙoƙarin da Uwargidan gwamnan ke yi wajen ci gaban mata da walwalar su da Yara da kuma ƙungiyoyi masu rauni a fadin Jihar Zamfara".

"Tun bayan hawanta mulki, Hajiya Huriyya Dauda Lawal ta nuna kyakkyawan shugabanci ta hanyar shirye-shiryen shiga tsakani na zamantakewa da kuma hulɗa da al'ummomin karkara, wanda hakan ya sa ta sami karramawa sosai a cikin jihar da wajenta.

A cikin jawabin ta, Uwargidan gwamnan ta nuna godiyar ta ga Sarkin Kudu, da Majalisar Masarautar Ɗansadau da kuma al'ummar Ɗansadau saboda wannan karramawa, inda ta bayyana hakan a matsayin girmamawa tare da dukkan masu ruwa da tsaki da suka himmatu wajen gina Jihar Zamfara.

Kyautar wannan karramawa ta nuna jajircewar Mai Martaba ga yin hidima tare da ƙarfafa ƙudurinta na ci gaba da fafutukar inganta rayuwar al'ummar Jihar Zamfara.
 

No comments