Daga Zubairu Lawal,Lafia Gwamna Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa ya bayyana cewa gwamnonin Arewa sun amince da sayen kayan aikin zamani na ...
Daga Zubairu Lawal,Lafia
Gwamna Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa ya bayyana cewa gwamnonin Arewa sun amince da sayen kayan aikin zamani na tsaro da kuma ɗaukar matasa aiki domin taimaka wa hukumomin tsaro wajen yaƙi da matsalolin tsaro a yankin.
Gwamnan ya bayyana haka ne yayin taron Majalisar Zartarwa ta Jihar da aka gudanar a Lafia, babban birnin jihar.
Gwamna Sule, wanda shi ne shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Arewa ta Tsakiya, ya ce an cimma wannan matsaya ne a taron da Kungiyar Gwamnonin Arewa da ta gudanar kwanan nan a Kaduna.
A cewar sa, Ƙungiyar Gwamnonin Arewa ta amince cewa kowace jiha za ta riƙa bayar da gudummawar naira biliyan daya (₦1bn) a kowane wata na tsawon shekara guda domin samar da kudaden tsaro da za su taimaka wajen shawo kan kalubalen tsaro a yankin.
Ya bayyana cewa kungiyar za ta gina babban ofishinta a Kaduna, kuma gwamnonin arewa goma sha tara sun bayar da gudummawar naira miliyan ɗari ɗaya (₦100m) kowanne, na tsawon shekara guda.
Gwamna Abdullahi Sule ya ƙara bayyana dalilan dakatar da harkar hakar ma’adinai a Jihar Nasarawa, inda ya ce wannan dakatarwar ba cikakkiyar hana aiki ba ce na tsawon watanni shida, sai dai dakatar da bayar da sabbin lasisi ne har sai an tantance masu hakar ma’adinai na gaskiya.
Ya ce wannan mataki ya zama dole sakamakon barazanar tsaro da ke tattare da bangaren hakhar ma"adanai wanda yasa ake bukatar tsuraran dokoki da zai inganta zaman lafiya a yan kunan da ake tsaron ma'a danai.

No comments