Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

DA UMI-ƊUMI: Shugaba Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Kimiyya Ta Azare Zuwa Jami’ar Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi

Daga Khalid Idris Doya  Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya canza sunan jami'ar kimiyyar lafiya mallakin gwamnatin tarayya da ke Azare zu...



Daga Khalid Idris Doya 

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya canza sunan jami'ar kimiyyar lafiya mallakin gwamnatin tarayya da ke Azare zuwa Jami'ar Sheikh Dahiru Usman Bauchi domin tunawa da marigayin. 

Tinubu ya misalta marigayin a matsayin babban malamin da ya hidimta wa addinin musulunci wanda ya yi aiki sosai domin Allah. 

Shugaban ƙasan ya tabbatar da cewa Sheikh Dahiru ya yi tasiri sosai wajen inganta harkokin ilimin al'ummar Bauchi da ma Nijeriya baki ɗaya. Kazalika, ya ce, magayin ya rungumi ɗa'a ta kwarai wanda ya yi amfani da rayuwarsa cikin dattako da kamala. 

Shugaban wanda ya kasance a jihar Bauchi a ranar Asabar domin jajanta wa iyalan mamacin tare da jajanta wa al'ummar jihar Bauchi bisa wannan rashin da suka yi, ya misalta rasuwar da cewa rashi ne babba ga ƙasar nan baki ɗaya. 

Tinubu, ya ƙara da cewa Shaikh Dahiru ya kasance mutum mai kima wanda ya sanya kishi da son Nijeriya a zuciyarsa. 

Shugaban ƙasan ya yi amfani da damar wajen kira ga al'umma da su ci gaba da yi wa kasar nan addu'an zaman lafiya da kwanciyar hankali, tare da bunƙasar tattalin arziki, ci gaba da rayuwa mai inganci. 

Ya yi addu'ar Allah ya jiƙan Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya sanya shi cikin aljanna maɗaukakiya.

Gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad ya nuna farin cikinsa da karancin da shugaban ƙasan ya yi wa iyalan Mamacin da kuma al'umman jihar tun daga lokacin rasuwar Sheikh Dahiru har zuwa yau da ya zo jihar da kansa domin jajantawa duk da tawagogin da ya yi ta turowa.

Da ya ke magana a madadin iyalan Marigayin su 820, Khalifansa Sheikh Ibrahim Shaykh Dahiru Usman Bauchi, ya ce tabbas ba za su taba mance mutumtawa da karancin da shugaban kasa ya musu ba. 

Dakta Bashir Sheikh Dahiru Usman Bauchi, shi ne ya miƙa saƙon a madadin Khalifan, ya ce tun ranar jana'izar mahaifinsu Tinibu ya turo tawaga ta musamman ƙarƙashin mataimakinsa Kashim Shettima domin halartar jana'izar daga baya kuma ya sake turo tawaga domin ta'aziyya, "Yau kuma ga shi da kansa ka zo domin jajanta mana gaskiya mun gode da wannan karamcin."

"A madadin dukkanin iyakokin Shaikh Dahiru Usman Bauchi su 820 da suka ƙunshi 'ya'ya 82 da ya rasu ya bar su a raye, mabiya da magoya baya sama da miliyan 63 tabbas muna miƙa godiya ta musamman ga shugaban kasa bisa karancin da ya yi ta nuna mana."

No comments