Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Shugaba Tinubu Ya Sha Alwashin Zurfafa Haɗin Gwiwa Da Ƙasashen Duniya Domin Murƙushe Barazanar Tsaro A 2026

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa gwamnatin sa za ta ƙara zurfafa haɗin gwiwa da ƙasashen yankin da na duniya a shekarar 2026,...


Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa gwamnatin sa za ta ƙara zurfafa haɗin gwiwa da ƙasashen yankin da na duniya a shekarar 2026, domin kawar da dukkan barazanar tsaro da ke barazana ga rayuka, dukiyoyi da kuma cikakken ikon ƙasar Nijeriya.

Shugaban ya bayyana hakan ne a jawabin saƙon sabuwar shekarar 2026 da ya gabatar ga ’yan Najeriya a ranar Alhamis.

Tinubu ya ce tafarkin gyara ƙasar na ba abu ne mai sauƙi ba, amma wajibi ne, yana mai jaddada cewa ci gaban tattalin arziki ba zai yi armashi ba tare da tsaro da zaman lafiya ba.

Ya ce Nijeriya na ci gaba da fuskantar barazanar ’yan ta’adda da masu aikata laifuka da ke ƙoƙarin dagula zaman lafiyar ƙasa, amma gwamnati na ɗaukar matakan da suka dace domin dakile su.

Shugaban ya bayyana wasu hare-hare da aka kai kwanan nan tare da haɗin gwiwar abokan hulɗa na ƙasa da ƙasa, ciki har da Amurka, domin raunana ƙungiyoyin ta’addanci.

A cewarsa, “A cikin haɗin gwiwa da abokan hulɗa na duniya, ciki har da Amurka, an ɗauki matakai masu ƙarfi kan wuraren ’yan ta’adda a wasu sassan Arewa maso Yamma a ranar 24 ga Disamba.”

Ya ƙara da cewa rundunonin tsaro na ci gaba da kai farmaki kan sansanonin ’yan ta’adda da ’yan fashi a yankunan Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas.

Tinubu ya bayyana cewa a shekarar 2026, hukumomin tsaro da na leƙen asiri za su ƙara ƙarfafa musayar bayanai da daidaita ayyuka da abokan hulɗa na yankin da na duniya, domin kawar da duk wata barazana ga tsaron ƙasa.

Ya sake jaddada ƙudirin gwamnatin tarayya na kare rayuka, dukiyoyi da cikakken ikon ƙasar Najeriya.

Game da gyaran tsarin tsaro, shugaban ya nuna goyon bayansa ga tsarin ’yan sanda na jihohi, tare da tanadin kariya da tsarin kula da masu tsaron dazuka cikin tsari da ɗa’a ga doka.

A ɓangaren tattalin arziki, Tinubu ya ce sabuwar shekarar za ta kawo wani sabon babi na bunƙasar tattalin arziki mai faɗi, wanda zai shafi rayuwar talakawa kai tsaye.

Ya sanar da cewa za a hanzarta aiwatar da shirin Renewed Hope Ward Development Programme, da nufin shigar da aƙalla ’yan Najeriya miliyan 10 cikin ayyukan samar da arziki.

A cewarsa, shirin zai bai wa aƙalla mutane 1,000 a kowace daga cikin unguwanni 8,809 na ƙasar damar samun aikin yi da dogaro da kai, ta fannoni kamar noma, kasuwanci, sarrafa abinci da ma’adinai.

Shugaban ya kuma tabbatar da cewa dukkan manyan ayyukan more rayuwa da ake yi a halin yanzu za su ci gaba ba tare da tsaiko ba.

Tinubu ya bukaci ’yan Najeriya su fahimci cewa gina ƙasa alhakin kowa ne, tare da ba da gudummawar sa domin cimma manufofin 2026.

A ƙarshe, ya yi addu’ar samun zaman lafiya, tsaro da kwanciyar hankali a ƙasar, yana mai fatan Allah ya kare ƙasa, ya kiyaye sojoji, tare da hallaka duk masu ƙoƙarin tayar da zaune tsaye.

Shugaban ya yi wa ’yan Najeriya fatan samun sabuwar shekara mai albarka, zaman lafiya da cigaba.
 

No comments