Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙara Ƙarfi A Watan Disamba, Yayin Da Malejin Hadahadar Kamfanoni Da Masana'antu Ya Kai Maki 57.6 – CBN

  Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya bayyana cewa saɓatta-juyattar ayyukan tattalin arziƙin cikin gida sun ci gaba da ƙarfafa a watan Disamba 2...


Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya bayyana cewa saɓatta-juyattar ayyukan tattalin arziƙin cikin gida sun ci gaba da ƙarfafa a watan Disamba 2025, yayin da malejin ƙarfin hadahadar masana'antu, wato 'Composite Purchasing Managers’ Index' (PMI) ya ci gaba da kasancewa sama da maki 50.  Hakan dai ke nan ya nuna irin yadda ake samun faɗaɗar ayyukan tattalin arziƙi.

Rahoton binciken PMI na watan Disamba 2025 da Babban Bankin ya fitar ya nuna cewa ƙarfin PMI ya kai maki 57.6, wanda ke tabbatar da samun bunƙasar tattalin arziki mafi ƙarfi da aka samu a kusan shekaru biyar da suka gabata.
Rahoton ya ce wannan ci gaba mai ɗorewa ya samo asali ne daga faɗaɗa ayyuka a manyan sassa da ke samar da ayyukan yi.

“Sakamakon PMI na ɓangarori ya nuna cewa harkokin noma da ayyukan gona ya ci gaba da ƙarfi da maki 58.5, masana’antu sun samu maki 57.0, yayin da ɓangaren ayyukan yau da kullum ya kasance a yanayi mai kyau da maki 51.9.
“Wannan yana nuna ci gaba mai yawa a ɓangaren kayan da ake fitarwa da ayyukan kasuwanci a cikin watan,” inji rahoton.

Binciken ya kuma nuna cewa sassa 32 daga cikin 36 da ake sa-ido a kan su sun samu ƙaruwa kamar a matakan sabbin odar kasuwanci da ayyukan yi.
A cewar wata sanarwa daga Hakama Sidi-Ali, Daraktar Rijo ta Sashen Sadarwa na Kamfanoni a CBN, ta ce wannan sakamako yana nuna dawowar buƙatar kayayyakin cikin gida a hankali da ƙarfafa ayyukan samarwa, musamman a ɓangaren tattalin arziƙin da ba na mai ba.
“Bankin ya danganta ƙarin ingantuwar PMI da tasirin kyawawan matakan da ake ɗauka na daidaita tattalin arziƙi, ciki har da ƙoƙarin inganta yanayin aiki da tsare-tsaren da ke gamsar da ’yan kasuwa tare da yin amanna da tsarin da ake a kai.

“Waɗannan gyare-gyaren sun ci gaba da ƙarfafa samar da ayyukan yi da kuma kyakkyawan fata game da makomar tattalin arziƙi a zangon ƙarshe na shekarar 2025,” inji ta.

Hakama ta ƙara da cewa bayanan PMI na watan Disamba ya ƙarfafa tsammanin tabbataccen yanayin ci gaban tattalin arziƙi yayin da Nijeriya ke shiga sabuwar shekara.
 

No comments