Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sake jaddada aniyar gwamnatinsa na tabbatar da aiwatar da hukuncin Kotun Ƙoli da ya bai wa ƙananan hukumo...
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sake jaddada aniyar gwamnatinsa na tabbatar da aiwatar da hukuncin Kotun Ƙoli da ya bai wa ƙananan hukumomi ’yancin karɓar kuɗaɗensu kai tsaye, ba tare da tsakura ba.
Shugaban Ƙasar ya bayyana hakan ne a daren Juma’a yayin taron Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC) karo na 15 na jam’iyyar APC, wanda aka gudanar a Cibiyar Taron Fadar Gwamnati da ke Abuja.
Tinubu ya gargaɗi gwamnonin jihohi da su bi umarnin Kotun Ƙoli, yana mai cewa rashin yin hakan na iya tilasta masa ɗaukar wasu matakan zartarwa. Ya ce, Kotun Ƙolin ta yi umarni a bai wa ƙananan hukumomi kuɗaɗensu kai tsaye, kuma gwamnatinsa na sa ido kan yadda ake aiwatar da wannan hukunci.
Shugaban Ƙasar ya kuma buƙaci shugabannin APC su ƙarfafa haɗin kai a cikin jam’iyyar, yana mai tuna musu cewa jam’iyyar ta ginu ne kan siyasar ci gaba, haɗa kowa da kowa, da mutunta bambancin ra’ayi. A cewarsa, dole ne a kasance masu haƙuri da juna domin dimokuraɗiyyar Najeriya ta dore.
Dangane da tsaro, Tinubu ya ce kafa ’yan sandan jihohi shi ne mafita, inda ya buƙaci Majalisar Dokoki ta Ƙasa da ta gayyaci Sufeto Janar na ’Yan Sanda domin duba hanyoyin samar da tsari da kariya daga cin zarafi. Ya ce hakan na da muhimmanci wajen yaƙi da ta’addanci da ’yan bindiga.
Shugaban Ƙasar ya kuma nuna goyon bayansa ga ƙoƙarin ƙara yawan mata a muƙaman zaɓe, tare da shawartar Majalisar Tarayya da ta guji ƙoƙarin mayar da harkar caca (lottery) ƙarƙashin ikon tarayya, yana mai cewa al’amarin ya rataya ne a hannun jihohi.
A nasa jawabin, Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya yabawa Tinubu bisa jajircewarsa da kwarewarsa ta siyasa, yana mai cewa duk wata haɗaka da za ta nemi kalubalantar Tinubu a zaɓen 2027 ba za ta yi nasara ba. Ya ce Tinubu ya taka muhimmiyar rawa wajen gina adawar siyasa a Najeriya tun kafin hawansa mulki.
Shi ma Shugaban APC na Ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya sanar da fara shirin rajistar mambobin jam’iyyar ta hanyar na’ura (e-registration) a dukkanin matakai, tare da roƙon shugabanni da masu ruwa da tsaki su ba da haɗin kai. Ya kuma sanar da tsawaita wa’adin kwamitocin jam’iyyar na matakai daban-daban har zuwa Maris 2026.
A ƙarshe, Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio da Gwamna Hope Uzodimma sun yaba wa Shugaban Ƙasar bisa tsare-tsaren gyaran tattalin arziƙi da suka ce na nufin bunƙasa tattalin arzikin ƙasa da walwalar al’umma.

No comments