Kowanne bangare na ƙasar nan zai amfana da yarjejeniyar kiwon lafiya da aka ƙulla tsakanin Nijeriya da gwamnatin Amurka. A cikin yarjejeniya...
Kowanne bangare na ƙasar nan zai amfana da yarjejeniyar kiwon lafiya da aka ƙulla tsakanin Nijeriya da gwamnatin Amurka.
A cikin yarjejeniyar ta Dala Biliyan 5.18 da aka rattaɓa wa hannu tsakanin ƙasashen biyu babu inda ke ɗauke da bayanin cewa mabiya addinin wani ɓangare ne kaɗai zasu amfana da wannan tsarin ƙarfafa kiyon lafiya.
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai Mohammed Idris, yayi wannan ƙarin haske ne yayin taron manema labarai na karshen shekarar 2025 a jiya Litinin, a Abuja.

No comments