Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Kungiyoyi Sun Yaba Wa Gwamnatin Kaduna kBisa Gyaran Cibiyoyin Lafiya na Matakin Farko (PHC) a Faɗin Jihar

Haɗakar ƙungiyoyin agaji da ƙungiyoyin fararen hula, tare da shugabannin addini, Sarakunan gargajiya da ƙungiyoyin kafafen yaɗa labarai sun ...

Haɗakar ƙungiyoyin agaji da ƙungiyoyin fararen hula, tare da shugabannin addini, Sarakunan gargajiya da ƙungiyoyin kafafen yaɗa labarai sun yaba wa Gwamnatin Jihar Kaduna bisa nasarar gyaran ɗaukacin cibiyoyin Lafiya na Matakin Farko (PHC) a faɗin jihar.

Haɗakar ta kai ziyarar tantancewa zuwa wasu zaɓaɓɓun cibiyoyin Kula da lafiya domin nuna godiya ga Gwamnatin Jihar Kaduna da Hukumar Kula da Lafiyar Matakin Farko ta Jihar bisa gyaran cibiyoyin Kula da lafiya guda 255 a cikin ƙananan hukumomi 23 na jihar.

Manufar ziyarar ita ce tantance tasirin sauye-sauyen da ake aiwatarwa a ɓangaren lafiya a matakin ƙasa-ƙasa da kuma yadda hakan ke amfanar mazauna karkara da birane.

Tawagar ta kasance ƙarƙashin jagorancin Fasto Dakta Yohanna Buru, Shugaban  Gidauniyar Farfaɗo da Sulhu ta Nijeriya watl  (Peace Revival and Reconciliation Foundation of Nigeria)

Tawagar ta haɗa da wakilan kafafen yaɗa labarai, waɗanda suka zagaya wasu daga cikin cibiyoyin lafiyar tare da lura da gagarumin ci gaba a fannin gine-gine, ingancin bayar da hidima, da kuma samuwar na’urorin kiwon lafiya na zamani.

Da yake jawabi yayin ziyarar, Fasto Dakta Buru ya bayyana gamsuwarsa da ingancin aikin da aka yi a cibiyoyin Kula da lafiyar da aka gyara, yana mai cewa sabbin gyare-gyaren za su taimaka matuƙa wajen inganta bayar da kiwon lafiya, musamman ga mata da yara.

Ya bayyana cewa haɗakar ta ga dacewar yin godiya ta musamman ga Gwamna Uba Sani saboda fifikon da ya bai wa lafiyar matakin farko da kuma sauyin da ake gani a fili a al’ummomi da dama a faɗin jihar.

Yace “Mun ga manyan sauye-sauye a cibiyoyin lafiyarmu, ciki har da samar da sabbin na’urorin kiwon lafiya. Waɗannan ci gaban sun kawo ingantaccen kiwon lafiya kusa da al’ummarmu, kuma mun zo ne domin nuna godiyarmu ga gwamnatin jihar,” 

Fasto Dakta Buru ya kuma yaba wa Hukumar Kula da Lafiyar Matakin Farko ta Jihar Kaduna bisa jajircewarta wajen inganta lafiya da walwalar mazauna jihar a shekarar 2025, yana mai tabbatar wa gwamnati da ci gaba da addu’o’i da goyon baya domin nasarar wannan gwamnati.

Haka nan, Madam Margaret Julius Kwada, wadda ta lashe lambar yabo ta Ranar Rashin Shan Taba ta Duniya sau huɗu daga Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) a Nijeriya, ta ce an shirya ziyarar ne tare da manyan masu ruwa da tsaki domin nuna godiya bisa gagarumin gyaran cibiyoyin Kula da lafiya a faɗin ƙananan hukumomi 24 na Jihar Kaduna.

Ta bayyana cewa shigar da na’urorin likitanci na zamani da ya ƙara ƙarfafa cibiyoyin lafiyar wajen bayar da ingantaccen sabis ga mata, yara da sauran rukunin da ke da rauni.

Ta kuma gode wa Gwamnan Jihar Kaduna bisa sauye-sauyen da ya kawo a dukkan ɓangarorin kiwon lafiya na jihar.

A nasa jawabin, Ambasada Idris Musa, mai rike da sarautar gargajiya daga Tudun Wada, Jihar Kaduna, ya yaba wa gwamnatin jihar bisa sauya cibiyoyin lafiyar al’umma zuwa na zamani, tare da samar da dakunan gwaje-gwaje da muhimman na’urorin kiwon lafiya.

Ya kuma yaba da sabuwar manufar gwamnatin jihar ta samar da motocin daukar marasa lafiya , yana mai bayyana hakan a matsayin babbar gudummawa ga inganta ayyukan gaggawa na kiwon lafiya a faɗin jihar.

Ya tabbatar wa gwamnati da ci gaba da addu’o’i domin nasarar shirye-shiryenta.

Da yake nasa jawabin a madadin gwamnati jihar Kaduna Babban Daraktan Hukumar Kula da Lafiyar Matakin Farko ta Jihar Kaduna, Farfesa Dakta Bello Jamoh Yusuf, ya gode wa haɗakar bisa ziyarar tare da jaddada aniyar jihar na ci gaba da ƙarfafa ayyukan lafiyar matakin farko.

Ya bayyana cewa Gwamnatin Jihar Kaduna na ɗaukar ma’aikatan lafiya sama da 1,800 domin cike gibin ma’aikata, tare da ƙara albashi ga ma’aikatan lafiya a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin ƙarfafa gwiwar ma’aikata.

Farfesa Yusuf ya shawarci mazauna jihar da su yi amfani da sabbin cibiyoyin  Kula da lafiya  da aka gyara, yana mai tabbatar musu da samun ingantaccen kiwon lafiya daga ƙwararrun ma’aikata tare da amfani da na’urorin bincike na zamani.

Ya kuma nuna godiyarsa ga ƙungiyoyin fararen hula, ƙungiyoyin agaji da na al’umma bisa ci gaba da goyon baya da haɗin kai a duk tsawon shekarar 2025, tare da yi wa mazauna jihar fatan shiga sabuwar shekara cikin nasara da albarka.




 

No comments