Rahotanni sun bayyana cewa ’yan bindigar da suka sace masu ibada a wani coci a jihar Kwara sun soma neman kuɗin fansa. 'Yan bindigar na ...
Rahotanni sun bayyana cewa ’yan bindigar da suka sace masu ibada a wani coci a jihar Kwara sun soma neman kuɗin fansa.
'Yan bindigar na neman a biya su dala dubu sittin da tara, kwatankwacin naira miliyan 100 kan kowane mutum.
A ranar Talata ne ’yan bindiga suka kai hari kan wani coci da ke ƙaramar hukumar Ekiti a jihar, inda suka kashe mutum biyu tare da sace mutane talatin da takwas.
Sace masu ibadar ya zo ne kwana guda bayan da wasu ’yan bindigar suka sace wasu ɗalibai mata fiye da ashirin a jihar Kebbi.
A daren Alhamis kuma wasu ’yan bindigar suka yi awon gaba da wasu gwamman ɗalibai da malamai a wata makarantar coci da ke garin Papiri a yankin ƙaramar hukumar Agwara.
Waɗannan hare hare dai na sake bayyana yadda matsalar tsaro ke addabar ƙasar, musamman ma arewaci.
.jpg)
No comments