Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamnatin Tarayya Ta Haramta Wa Jami’o’i Bai Wa Jami'an Gwamnati Digirin Girmamawa

Gwamnatin Tarayya ta kafa sabon doka da ta haramta wa jami’o’in ƙasar bai wa duk wani ɗan siyasa ko mai riƙe da muƙamin gwamnati digirin gir...



Gwamnatin Tarayya ta kafa sabon doka da ta haramta wa jami’o’in ƙasar bai wa duk wani ɗan siyasa ko mai riƙe da muƙamin gwamnati digirin girmamawa, domin dalile yadda ake karkatar da wannan girmamawa zuwa hanyar neman kuɗin shiga.

Hukumar Kula da Jami’o’i ta Ƙasa (NUC) ce ta sanar da hakan, inda ta nuna cewa binciken da ta gudanar ya gano makarantu 32 da ke aiki a matsayin masana’antar rabon digirin girmamawa, ciki har da jami’o’in ƙasashen waje goma da ba su da tantancewa, da kuma wasu jami’o’in cikin gida huxu marasa lasisi.

Sakatare Janar na NUC, Farfesa Abdullahi Yusufu Ribadu ne ya bayyana haka a Abuja yayin karɓar rahoton kwamitin da aka tura don bincikar yadda ake bayarwa da kuma amfani da digirin girmamawa ba bisa ka’ida ba a fadin ƙasa. Ya ce hukumar za ta fara kai farmaki kan duk wata cibiyar da ke ba da takardun bogi, tare da hadin guiwar hukumomin tsaro da sauran hukumomin gwamnati.

Ribadu ya yi gargaɗi mai tsanani ga mutanen da ke fitowa a bainar jama’a suna kiran kansu “Dr” bayan sun samu digirin girmamawa, ba tare da amfani da cikakkiyar nomanqlature ba kamar Doctor of Literature (Honoris Causa) ko D. Litt. (h.c.). Ya ce duk wanda ya saba wa wannan doka zai fuskanci gurfanarwa.

Ya ƙara da cewa an kebe digirin girmamawa ne domin girmama wani da ya yi abin a yaba wa al’umma ba tare da yana riƙe da mukamin gwamnati ba, yana mai misalta digirin girmamawa da Jami’ar Nile ta ba tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan shekaru goma bayan saukarsa daga mulki a matsayin abin koyi.

Ribadu ya nanata cewa jami’o’in gwamnati da na ‘yan ƙasuwa da aka amince da su kawai ne ke da ikon ba da irin wannan digiri, kuma masu karɓa dole su bi tsarin sunan da doka ta tanada, maimakon amfani da taken “Dr” wanda na masu digirin ilimi ne na zahiri ko na likitanci.

Rahoton ya kuma tabbatar da cewa akwai kungiyoyi 15 da ke kiran kansu cibiyoyin bai wa mutane digiri duk da cewa ba su da lasisi, sannan akwai cibiyoyi uku da ba su da wata alaqa da bayar da digiri amma suna yin hakan a boye.

Ya ce matakin da NUC ke dauka yanzu shi ne tsabtace fannin gaba ɗaya, domin dakatar da yawaitar cin zarafi da gurbata darajar digirin girmamawa a Nijeriya.

No comments