Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta musanta rahotonnin da ta ce ana yaɗawa da ke cewa ta umarci a rufe makarantu a faɗin ƙasar daga ranar Litinin...
Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta musanta rahotonnin da ta ce ana yaɗawa da ke cewa ta umarci a rufe makarantu a faɗin ƙasar daga ranar Litinin mai zuwa.
Cikin wata sanarwa, ma'aikatar ilimi ta ce rahoton ba gaskiya ba ne.
"Rahoton ba daga gwamnatin tarayya yake ba, ko ma'aikatar ilimi, ko wata ma'aikatar ilimi ta jiha, ko wata hukumar tsaro," inji sanarwar.
A jiya Juma'a ne gwamnatin Najeriyar ta sanar da rufe makarantun sakandare na kwana 41 mallakarta da ake kira Unity Schools a faɗin ƙasar.
Umarnin na zuwa ne bayan sace ɗalibai mata 25 a jihar Kebbi da kuma wasu 315 a jihar Neja a ranakun Litinin da kuma Juma'a.

No comments