Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Jami’an Tsaro Sun Ceto Mata Da Yara 25 Daga Hannun ’Yan Ta'adda A Zamfara

Gwamnatin Jihar Zamfara ta samu yabo da jinjinawa bayan da jami’an rundunar ’yan sanda suka yi gagarumin nasarar ceto mata da yara 25 da ’ya...




Gwamnatin Jihar Zamfara ta samu yabo da jinjinawa bayan da jami’an rundunar ’yan sanda suka yi gagarumin nasarar ceto mata da yara 25 da ’yan fashi suka yi garkuwa da su a ƙauyen Kuraje, cikin ƙaramar hukumar Gusau.

A cewar Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, DSP Yazid Abubakar, maharan sun kutsa ƙauyen ne suka tafi da mata 10 tare da ’ya’yansu 15, lamarin da ya tayar da hankula a yankin. Sai dai cikin gaggawa, rundunar hadin guiwa ta Damba da Gusau ta samu kiran gaggawa, inda nan take suka afkawa maharan a dajin da suka tsere zuwa.

DSP Abubakar ya ce bayan artabu da jami’an tsaro suka yi da ’yan bindigar, an yi nasarar ceto dukkanin mutanen cikin koshin lafiya, inda aka kaisu Sabon Garin Damba domin ci gaba da tantancewa da kula da lafiyarsu.

Wannan nasara ta sake tabbatar da matakan gaggawa da sabbin dabarun tsaro da gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dauda Lawal ta ke ɗauka wajen karya lagon ’yan bindiga da dawo da zaman lafiya a Zamfara.

A cikin makonnin da suka gabata, gwamnatin jihar ta ƙara haɗa kai da hukumomin tsaro, tare da ƙarfafa rundunonin hadin gwiwa a yankunan da abin ya fi ƙamari. Wannan ya taimaka wajen samun saurin mayar da martani kamar yadda ya faru a Kuraje.

Lamarin ya faru ne a daidai lokacin da ake ci gaba da fargaba kan sace ɗalibai a makwabtan jihohi – Kebbi da Neja – abin da ya sa jama’a ke yaba irin jajircewar da gwamnatin Zamfara ta nuna wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Mutanen yankin sun bayyana jin dadinsu da godiyarsu ga jami’an tsaro da gwamnatin jihar bisa wannan nasarar da suka kira “warwatse barazana da kuma kara ɗaga murya kan cewa Zamfara na kan hanyar dawo da cikakken zaman lafiya.”

Gwamnatin jihar ta tabbatar da cewa ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen ƙara karfafa rundunonin tsaro domin ganin an ci gaba da fatattakar miyagu a kowane sashi na jihar.

No comments