Daga Zubairu Lawal, Lafia Wata ƙungiyar mai suna 'Architect Shehu Ahmed Tukur Vanguard (ASAT),' wacce ta ƙunshi mutane daga Ƙanana...
Daga Zubairu Lawal, Lafia
Wata ƙungiyar mai suna 'Architect Shehu Ahmed Tukur Vanguard (ASAT),' wacce ta ƙunshi mutane daga Ƙananan Hukumomi biyar na mazabar Nasarawa ta Kudu, ta bayyana cewa takarar kujerar Gwamnan jihar Nasarawa a jam'iyyar APC ta Shehu Tukur ce.
Wannan yana ƙunshe ne cikin jawaban da wasu masu jawabi a wani gangami na musamman a aka shiylrya a Lafia, inda suka bayyana cewa bisa ɗimbin gudumawar da Tukur ke bayarwa ga al’umma ya sa shi cancanta ya tsaya neman kujerar gwamnan jiharNasarawa.
Ɗaya daga cikin masu jawabin, Yahaya Mirror daga Ƙaramar Hukumar Doma ya ce Gwamna Abdullahi Sule yana tafiyar da jihar cikin sauyi, don haka akwai buƙatar wanda zai gaji tafiyar sa ya ci gaba da gina jihar.
“Dalilin mu na neman Architect Tukur ya tsaya takarar kujerar gwamnan jihar ya samo asali ne daga jajircewar sa da irin gudumawar da yake bayarwa wajen gina jihar. Saboda haka, muna roƙon Tukur da ya amsa kiran mu ya tsaya takara a ƙarƙashin jam’iyyar APC,” in ji Mirror.
Ya ce amincewar Tukur ya tsaya takarar za ta bai wa jama’ar jihar ƙwarin gwiwar ci gaba da aiwatar da manyan ayyukan da gwamnatin Abdullahi Sule ta fara.
Shi ma Adamu Oyiko daga Doma ya bayyana cewa jama'ar yankin sa na buƙatar ingantaccen shugabanci, kuma Architect Tukur ne a saman jerin mutanen da suka dace su jagoranci jihar.
“Addu’ar mu da fatan mu shi ne Architect Ahmed Shehu Tukur ya amsa kiran da Nasarawa ta Kudu ta yi masa, ba wai kawai ya tsaya takara ba, har ma ya gaji Gwamna Abdullahi Sule a matsayin gwamnan Nasarawa.”
Wani mamban ASAT daga Keana, Umar Dalhatu Abubakar, ya ce Architect Tukur jarumi ne mai jajircewa wanda zai iya kai jihar mataki na gaba.
A nasa bangaren, shugaban ASAT na jiha, Abdullahi Yamani, ya bayyana cewa Architect Tukur yana cikin mutanen da ke gina jihar tun kafuwarta a 1996.
“A matsayin sa na Architect, Tukur ya yi aiki tare da sojoji da gwamnoni na farar hula wajen zayyana da gina muhimman gine-gine da suka kai jihar matsayinta na yau. Saboda haka, yana da cikakken ilimi game da cigaban jihar, kuma yana da kwarewa da zai jagoranci jihar bisa hanyar cigaba,” in ji Yamani.
Yamani ya yi alƙawarin cewa ba za su gaji ba wajen ci gaba da kira da kuma lallashin Tukur da ya amince ya tsaya takara don ci gaba da gina jihar.
Gangamin ya kuma ƙunshi nune-nunen rawa na al'adu daga ƙungiyoyi daban-daban na jihar.

No comments