Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Dalilan Kafa Ƙungiyar Sullubawa Ta Kano

 Daga Ibrahim Muhammad, Kano An samar da ƙungiyar Sullubawa ne don wayar da kan dukkan Fulani na cikin gari da makiyaya akan samun ilimi na ...


 Daga Ibrahim Muhammad, Kano

An samar da ƙungiyar Sullubawa ne don wayar da kan dukkan Fulani na cikin gari da makiyaya akan samun ilimi na addini dana zamani da sanin muhimmancin abin da ya shafi rayuwa gaba ɗaya.

Shugaban Ƙungiyar na ƙasa Usman Muhammad Garba ne ya bayyana hakan da yake zantawa da 'yan jarida bayan taron da suka gudanar a babban ɗakin karatu na Kano.

Ya ce suna nusar da 'yan'uwa makiyaya kan muhimmancin zama waje ɗaya don barin yawon  ƙaura na jeji da ake yi da shanu, saboda yanzu yanayi ya canza, ba wuraren kiwo kuma zaman lafiya ya zama abin da ya zama. Dalilin wannan makiyayi na iya zuwa ma ya rasa dukiyar sa baki ɗaya a matsayin Bafulatani da bai san wata sana'a ba da ta wuce kiwo.

Ya ce suna wayar da kan Fulani muhimmancin su sami wurare su saya su zauna wuri ɗaya a yi musu makarantu da Asibitoci da abubuwa na inganta jin daɗin rayuwa, suna kuma nuna musu muhimmancin zaman lafiya tsakanin su da  manoma da musamman irin wannan lokaci na dawowar shanu daga wurin mashekari, ana samun hatsaniya da rashin haƙuri ke jawowa.

Shugaban ƙungiyar ta Sullubawa na ƙasa, Usman Muhammad Garba ya ce sun sami nasarar haɗin kan al'umma a dalilin kafa ƙungiyar da amsa kiraye-kirayen da ta ke yi, kama daga ilimi,iyaye suna sa yara a makarantu suna ma ƙirƙirar makarantun da kansu na addini dana zamani a rugage suna biya ana koyar da ƴaƴansu ba sa jiran Gwamnati.

Ya ce sun samu nasarar fahimtar da Fulani hukumar 'yan sanda da sauran jami'an tsaro an yi su ne don kare al'umma, ba an yi su ba ne don su cutar da su,  suna aiki ne don kare dukiya da rayuka, suna wayar da kai kuma Fulani suna fahimtar hakan.

Sai dai ya nuna damuwa na cewa a bangaren Shugabanin Ƙananan Hukumomi ba sa samun goyon baya sosai, don ya kamata Sarakunan Fulani a ce duk wani abu da Gwamnatin ke yi ya zama ana yin sa da su, kuma duk wata tattaunawa ta tsaro ya zama ana yi da su domin su san su ma mutane kamar kowa, amma ana  wofintar  da su.

Daga nan sai Shugaban ya  yaba wa Gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf da cewa su  Fulani babu abin da za su ce masa sai dai addua Allah ya sa ya gama lafiya ya sake maimaitawa karo na Biyu, domin wani dukkan wani tsari na kyautatawa da jawo al'ummar su a jiki, Fulani  babu abin da suka rasa.

No comments