Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

KULA DA KIWON LAFIYA: Ma'aikatan Jinya A Jihar Kaduna Sun Jinjina Wa Gwamna Uba Sani

A wani taron manema labarai da suka kira a ofishin Kwamishinan yaɗa labarai, gamayyar ƙungiyoyin ma'aikatan lafiya da ke aiki a jihar Ka...


A wani taron manema labarai da suka kira a ofishin Kwamishinan yaɗa labarai, gamayyar ƙungiyoyin ma'aikatan lafiya da ke aiki a jihar Kaduna, sun yaba wa Gwamna Uba Sani bisa gyara da inganta harkar kiwon lafiya a duk faɗin jihar.

Gamayyar ma'aikatan lafiyar, waɗanda suka haɗa da ƙugiyar Likitoci ta ƙasa, reshen jihar Kaduna, da ta asibitin koyarwa na Barau Dikko, ƙungiyar ma'aikatan jinya da Unguwar-zoma (NANNM), ma'aikatan lafiya fannin binciken cututtuka, tare da dukkan ƙungiyoyin harkar lafiya da ke Kaduna, sun jinjjna wa Gwamnan bisa irin kulawar da ya ke bayarwa ga harkar lafiya ta kowane fanni a jihar.

Suka ce, "Mun kira ku wannan taron manema labarai ne a ƙarƙashin waɗannan ƙungiyoyi domin mu yi jinjina, tare da yabo bisa irin sauye-sauyen da ake samu a harkar kiwon lafiya a ƙarƙashin jagoran Gwamna Sanata Uba Sani, CON"

Ma'aikatan lafiyar suka ci gaba bayyana cewa, "Muna matuƙar jinjina ga mai girma Gwamna bisa fara aiwatar da kashi 100 na tsarin albashin ma'aikatan lafiya (CONMESS) na 2024. Sannan kuma ga amincewar da ya yi na tsabar kuɗi ₦518,628,393.68 duk wata, da kuma ₦6,223,540,724.16 kowace shekara ga ma'aikatan lafiya da ke jihar."

Haka kuma ƙungiyar ta miƙa godiyar ta ga Gwamna Uba Sani bisa amincewar da ɗaukar ɗaliban da suka kammala karatun aikin kiwon lafiya daga Jami'ar jihar Kaduna nan take, wanda suka ce wannan ba ƙaramin ƙarin zaburantawar ba ne ga harkar lafiya a jihar.

Ma'aikatan harkar lafiyar, ba su kammala jawabin su ba, sai da suka zayyano ƙarin wasu abubuwan da suka gani gwamnan ya cancanci yabo a kai, waɗanda suka haɗa da kammala ginin asibitin ƙwararru mai gadaje 300, sannan ga ayyukan da ake gudanarwa na gyaran manyan asibitoci guda 15.

Sauran sun haɗa da ɗaga darajar asibitocin sha-ka-tafi guda 200 zuwa matsayi 2. Sannan kuma ga samar da na'urar iskar gas ta marasa lafiya a kowanne yankin Sanata na jihar, tare da samar da asibitocin ƙwararru na yara gida ɗaya a kowene yanki, tare da sauran abubuwan yabo da dama.

Cikin waɗanda suka sanya hannu a takardar menama labaran, sun haɗa da shugaban ƙungiyar ƙwadago (NLC) ta jihar Kaduna, Kwamared Ayuba Suleiman, Dr Bayero Samuel na ƙungiyar Likitoci da ƙasa (NMA), Kwamared Ibrahim Dodo Enock na gamayyar ƙugiyoyin kiyon lafiya  (JEHESU) da sai sauran su.

 

No comments