Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

SATA A AMURKA: FBI Ta Saka Tukuicin Dala 10,000 Kan Ɗan Nijeriya

Hukumar Binciken Manyan Laifuffuka ta Amurka (FBI) ta sanya ladar Dala 10,000 a neman da take yi wa wani ɗan asalin Nijeriya. Hukumar FBI ta...



Hukumar Binciken Manyan Laifuffuka ta Amurka (FBI) ta sanya ladar Dala 10,000 a neman da take yi wa wani ɗan asalin Nijeriya.

Hukumar FBI ta sanya kuɗin ne ga duk wanda ya bayar da bayanan da za su kai ga kama Olumide Adebiyi Adediran, ɗan asalin Nijeriya mai shekara 56.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da hukumar FBI ta sanya a shafin X a ranar Laraba, 24 ga watan Satumban 2025.

Ana neman Olumide Adebiyi Adediran ne saboda zargin yin damfara ta banki a Amurka.

A cewar FBI, Adediran ya yi amfani da bayanan sata na ‘yan ƙasar Amurka wajen buɗe asusun banki da kuma asusun cire kuɗi.

A sanarwar, hukumar FBI ta ce wanda ake nema ya shiga wani banki a Champaign, jihar Illinois, inda ya yi ƙoƙarin cire kuɗi daga wani asusu.

FBI ta ce Adediran ya tsere daga jihar Illinois a ƙarshen watan Disamba, 2001, jim kaɗan kafin a fara shari’ar sa kan zarge-zargen damfara ta banki, damfarar bayanan ƙarya da kuma damfara ta katin cire kuɗi.

Daga bisani, a ranar 2 ga Janairu, 2002, kotu ta bayar da sammacin kama shi saboda karya sharuɗɗan beli.

"Ana neman Olumide Adebiyi Adediran bisa karya sharuɗɗan beli. A watan Agusta, 2001, ya shiga banki a Champaign, Illinois, inda ya yi kokarin cire kuɗi daga asusun ajiya na banki."

"Haka kuma, ana zargin ya yi amfani da bayanan sata na na ‘yan ƙasar Amurka wajen buɗe asusun banki da cire kuɗi."

"Adediran ya tsere daga yankin 'Central District of Illinois' a ƙarshen watan Disamba, 2001, kafin fara shari’ar sa a kan laifuffukan damfara da ake zargin sa da su."

"An bayar da takardar sammacin kama shi a ranar 2 ga Janairu, 2002, bayan tuhumar sa da karya sharuɗɗan beli."

Hukumar ta buƙaci duk wanda ke da bayani game da wanda ake nema da ya tuntubi ofishin FBI mafi kusa da shi, ko kuma ya kai rahoto ga ofishin Jakadancin Amurka mafi kusa.

No comments