Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Za Mu Ɗauki Mataki Kan Lawan Triumph Bayan Sanun Ƙorafi – Gwamnan Kano

Wasu mazauna birnin Kano sun yi zanga-zangar lumana game da zargin malamin addini Sheikh Lawan Abubakar Triumph da kausasa kalamai kan Annab...



Wasu mazauna birnin Kano sun yi zanga-zangar lumana game da zargin malamin addini Sheikh Lawan Abubakar Triumph da kausasa kalamai kan Annabi Muhammadu (SAW).

Masu zanga-zangar sun dangana da farfajiyar gidan gwamnatin Kano, inda Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tarɓe su tare da yi musu jawabi.

A baya-bayan nan ne aka ga malamin a wani bidiyo yana musanta batun cewa haihuwar Annabi da kaciya, kamar yadda wasu litattafai suka ruwaito, ba karama ba ce saboda "ana iya haihuwar sauran mutane ma da kaciyar".

A cewar malamin, karama na nufin "wani abin al'ajabi da Allah yake bai wa annabawa su kaɗai". Kazalika, malamin ya ce ruwayoyin ba su inganta ba.

Gwamna Abba ya umarci masu ƙorafin da su kwantar da hankali, inda ya nemi su rubuto masa takardar koke a hukumance ta hannun ofishin sakataren gwamnati.

"In Allah ya yarda za mu ɗauki matakin da bai saba wa Shari'a ba," inji gwamnan.

"Abin da nake so shi ne ku koma ku rubuto wa gwamna takarda, wadda ita ce za a yi amfani da ita daga nan har zuwa ƙolin ƙoli."

Masu ƙorafin sun amince su kai wa gwamnan takardar da ya nema da misalin ƙarfe 10:00 na safiyar gobe Alhamis. 

No comments