Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya taya tsohon ƙaramin ministan gidaje da ci gaban birane, Alhaji Abdullahi Tijjani Gwarzo, murnar zagayowar r...
Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya taya tsohon ƙaramin ministan gidaje da ci gaban birane, Alhaji Abdullahi Tijjani Gwarzo, murnar zagayowar ranar haihuwarsa ta cika shekaru 65.
A cikin wata sanarwa da mai ba shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ya fitar, Shugaba Tinubu ya yaba da kishin ƙasa da kuma jajircewar Alhaji Gwarzo a harkokin siyasa, musamman a ɓangaren manufofin ci gaban al’umma.
Shugaban ya ce ƙaunar da jama’a ke nuna wa Gwarzo ya samo asali ne daga siyasar gaskiya da rikon amana da ya yi, tun daga lokacin da ya yi shugabancin ƙaramar hukuma har zuwa lokacin da ya zama mataimakin gwamnan Jihar Kano tsakanin shekarar 2007 zuwa 2011.
Ya ƙara da cewa a shekarar 2011, lokacin da Gwarzo ya tsaya takarar gwamnan Kano a ƙarƙashin jam’iyyar Action Congress of Nigeria (ACN), ya taka muhimmiyar rawa wajen ƙarfafa dangantakar siyasa da daga bisani ta samar da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a shekarar 2013.
Shugaba Tinubu ya yi masa fatan alheri da kuma ƙarfafa ma sa kan ya ci gaba da sadaukarwar sa wajen bautar ƙasa.
No comments