Gwamnan Babban Bankin Nijeriya, Olayemi Cardoso ya bayyana cewa zuwa yanzu manyan bankuna 14 ne suka cika sharaɗin tabbatar da cewa ƙarfin ...
Gwamnan Babban Bankin Nijeriya, Olayemi Cardoso ya bayyana cewa zuwa yanzu manyan bankuna 14 ne suka cika sharaɗin tabbatar da cewa ƙarfin jarin kowanen su kada ya gaza kai Naira Biliyan 500.
Cardoso ya bayyana haka ne a ranar Talata, yayin zantawa da manema labarai bayan kammala taron kwanaki biyu na Kwamitin Ƙwararrun Mashawartan Tattalin Arzikin Ƙasa, a Abuja.
Tun cikin watan Maris ne dai CBN ya kafa sharaɗin cewa duk wani babban bankin da ke da rassa a ƙasashen waje, tilas mafi ƙanƙantar jarin sa ya kasance Naira biliyan 500 lakadan ba ajalan ba.
A taron na ranar Talata, wanda shi ne na 302 da CBN ya shirya, tun bayan kafa bankin, Cardoso ya yi kira ga bankunan kasuwanci su ci gaba da hoɓɓasan ƙarfafa jarin su, domin kai ga nasarar bunƙasa tattalin arzikin ƙasa.
Har ila yau a wurin taron dai Babban Bankin Nijeriya ya rage kuɗin ruwan da bankuna ke caza daga kashi 27.5 zuwa kashi 27.
Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya bayyana rage kuɗin ruwa, daga kashi 27.5 zuwa kashi 27.
Gwamnan CBN Olayemi Cardoso ne ya bayyana haka, a ranar Litinin jim kaɗan bayan kammala taron Kwamitin Ƙwararrun Bada Shawarwari kan Tattalin Arziki (MPC), a Abuja.
Cardoso ya ce kwamitin ya amince a rage kuɗin ruwa da ɗigo .50, wato daga kashi 27.5 bisa 100, ya koma kashi 27 bisa 100.
Wannan ne dai karo na farko da adadin gejin kuɗin ruwa ya yi ƙasa, wato mafi ƙaranci a cikin shekaru biyar.
Gwamnan na CBN ya ce an yanke shawarar rage kuɗin ruwan ne domin ci gaba saukar malejin tsadar rayuwa da na hauhawar farashi, wanda tsawon watanni biyar kenan ake samu a jere.
Dama masara sun yi hasashen cewa malejin tsadar rayuwa zai ƙara yin ƙasa sosai a sauran watannin ƙarshen 2025.
Haka kuma wani dalilin rage kuɗin ruwan shi ne domin a ci gaba da ƙarfafa tattalin arziki.
Wannan ragin kuɗin ruwa da CBN ya yi wanda bankuna za su riƙa cajin masu karɓar ramce, ya zo ne daidai lokacin da ita kuma Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) ta ce tattalin arzikin Nijeriya ya ƙaru da kashi 4.23 cikin ɗari a darajar GDP a zango na biyu na shekarar 2025, idan aka kwatanta da shekarar 2024.
Hukumar ta bayyana haka ne a cikin rahoton GDP na Nijeriya na zango na biyu na shekarar 2025 da ta fitar a Abuja, a ranar Litinin.
Rahoton ya nuna cewa wannan ci gaban ya fi kashi 3.48 da aka samu a zango na biyu na 2024, haka kuma ya fi kashi 3.13 da aka samu a zangon farko na 2025.
No comments