Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Nijeriya Ta Jaddada Matsayar Ta Na Tabbatar Da Yancin Ƙasar Falasɗinu A Majalisar Ɗinkin Duniya

Gwamnatin Tarayya ta Nijeriya ta bayyana cewa, mafita ta samar da ƙasashe biyu ita ce hanya mafi kyau da za ta kawo dawwamammen zaman lafiya...


Gwamnatin Tarayya ta Nijeriya ta bayyana cewa, mafita ta samar da ƙasashe biyu ita ce hanya mafi kyau da za ta kawo dawwamammen zaman lafiya ga al’ummar Falasdinu.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wanda Mataimakin sa, Kashim Shettima, ya wakilta, ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a babban taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 80 a birnin New York.

Tinubu ya ce: “Ba mu yarda da ganin rayuwar ɗan Adam ta makale cikin jayayya marar ƙarewa ba. Shi ya sa muke tsayawa ba tare da shakka ba, muna cewa mafita ta samar da ƙasashe biyu masu yancin kan su ita ce hanya mafi kyau ga zaman lafiya a Falasdinu.”

Ya ƙara da cewa da daɗewa al’ummar Falasɗinu suna fuskantar rikice-rikicen da suka jawo zubar da jini da tashin hankali.

“Ba mu zo a matsayin masu ɓangaranci ba, mun zo ne a matsayin masu burin kawo maslaha. Mun zo a matsayin ‘yan uwa a duniyar da bai kamata ta rage darajar rayuwa ta mutum ɗaya zuwa wani abin wasa a siyasa ba.”

Shugaban ya bayyana cewa mutanen Falasdinu ba “ƙurar rikici” ba ce, su ma ‘yan Adam ne kamar kowa da kowa, masu daraja da ‘yancin rayuwa irin wanda sauran mutane ke morewa.

Ya jaddada cewa Nijeriya na goyon bayan ƙimar zaman lafiya da haɗin kai a maimakon tashin hankali, ramuwar gayya da zubar da jini.

Tinubu ya ce, Nijeriya za ta ci gaba da yin aiki ta hanyar dandalin haɗin gwiwa na ƙasa da ƙasa don ƙarfafa doka da samar da amincewa tsakanin ɓangarorin dake hamayya.

Dangane da al’amuran cikin gida kuma, shugaban ya ce Najeriya ta ɗauki matakai masu wahala don sake fasalin tattalin arziki da kawar da tallafin man fetur da kuma tsarin canjin kuɗi, domin a samu ci gaba da bunƙasar tattalin arzikin da zai kawo zaman lafiya mai dorewa.
 

No comments