Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Matashi Ya Kashe Kakannin Sa Da Wuƙa Kan Taƙaddamar Abinci A Kano

A yau Alhamis ne wani mutum mai suna Mutawakilu Ibrahim mai shekaru 30 a duniya ya daba wa kakanin sa wuƙa har lahira sakamakon wata taƙadda...



A yau Alhamis ne wani mutum mai suna Mutawakilu Ibrahim mai shekaru 30 a duniya ya daba wa kakanin sa wuƙa har lahira sakamakon wata taƙaddama da ta kaure a tsakanin su kan abinci.

An ruwaito cewa lamarin ya auku ne a Ƙofar Dawanau cikin birnin Kank da misalin ƙarfe 9:30 na safiyar ranar 25 ga watan Satumbar nan 2025, ya jefa al’umma cikin firgici da alhini.

A wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta fitar ta ce, waɗanda harin ya rutsa da su, Muhammad Ɗansokoto mai shekaru 75 da Hadiza Tasidi mai shekaru 65, an kai musu hari ne a gidan su, inda ‘yan sandan suka bayyana a matsayin rashin jituwa kan abinci.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Abdullahi Kiyawa, ya ce wani mazaunin yankin da abin ya shafa ne ya kai rahoton lamarin ga hedikwatar ‘yan sandan da ke Dala wanda ya shaida yadda rikicin ya faru.

“A yayin rikicin, wanda ake zargin ya yi amfani da wuƙa wajen daba wa dukkan mutanen biyu a sassa daban-daban na jikin su, wanda hakan ya jawo munanan raunuka.

Nan take aka garzaya da tsofaffin ma’auratan zuwa asibitin ƙwararru na Murtala Muhammad da ke Kano, inda jami’an lafiya suka tabbatar da rasuwar su,” in ji Kiyawa.

Mazauna yankin Ƙofar Dawanau sun bayyana kisan a matsayin abin takaici da kuma tada hankali.

Wasu shaidun gani da ido sun shaida wa manema labarai cewa, ma’auratan na mutunta su sosai a yankin kuma sun shafe shekaru da dama suna zaune lafiya.

"Sun kasance masu kirki da mutunci kuma kowa yana ƙaunar su. Babu wanda ya taba tunanin za su mutu a haka, musamman a hannun jikan su," in ji wani maƙwabcin su.

Rundunar ‘yan sandan ta tabbatar da cewa an kama Ibrahim tare da tsare shi domin ci gaba da bincike.

Rundunar ‘yan sandan ta tabbatar wa da jama’a cewa za a yi adalci, tare da jaddada cewa za a gudanar da shari’ar cikin gaggawa idan aka yi la’akari da girman laifin.

“Kwamishinan ‘yan sanda, Muhammad Usaini Gumel, ya bayar da umarnin gudanar da bincike na gaskiya kan lamarin, wanda ake zargin za a gurfanar da shi a gaban kotu bayan kammala bincike,” in ji Kiyawa.

No comments