Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya sake jaddada buƙatar a bai wa Nijeriya kujerar dindindin a Kwamitin tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya, a matsay...
Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya sake jaddada buƙatar a bai wa Nijeriya kujerar dindindin a Kwamitin tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya, a matsayin ɓangare na sauye-sauyen da ake son yi wa tsarin majalisar.
Tinubu, wanda Mataimakin sa, Sanata Kashim Shettima, ya wakilta, ya yi wannan kira ne a lokacin da yake jawabi a zauren tattaunawa na babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 80 a birnin New York.
“Ya zama dole Nijeriya ta samu kujerar dindindin a Kwamitin tsaro. Wannan wani muhimmin ɓangare ne na sauye-sauye domin dawo da amincewa ga wannan hukuma, wacce ita ce ginshikin tsarin haɗin gwiwa na duniya,” in ji shi.
Shugaban ya ce Majalisar Dinkin Duniya za ta dawo da martabarta ne kawai idan ta dace da yanayin duniya na yanzu, ba ta bar tarihi ya daure ta ba.
Ya bayyana cewa lokacin da aka kafa Majalisar Dinkin Duniya, Nijeriya ƙasa ce ƙarƙashin mulkin mallaka mai mutane miliyan 20, ba tare da samun wakilci a teburin da ake yanke hukunci kan makomarta ba.
“Yanzu kuwa, mu ƙasa ce mai ‘yanci, muna da fiye da mutane miliyan 236, kuma an yi hasashen nan da shekaru masu zuwa mu zama ƙasa ta uku mafi yawan jama’a a duniya.
Nijeriya ta daɗe tana zama ginshiƙin tsaro a nahiyar Afirka, kuma abar dogaro a aikin kiyaye zaman lafiya na duniya,” in ji Tinubu.
Ya bayyana cewa sojojin Nijeriya sun taka rawa a cikin ayyuka 51 daga cikin 60 na kiyaye zaman lafiya da Majalisar Ɗinkin Duniya ta gudanar tun bayan samun ‘yancin kai a 1960.
Shugaban ya kuma ce ƙasar ba ta tsaya ga kanta ba wajen yakar ta’addanci, inda ta yi aiki tare da makotan ƙasashen Afirka ta hanyar Multinational Joint Task Force (MNJTF).
Tinubu ya ce Najeriya ta koyi darasi daga doguwar gwagwarmaya da ta yi da ƙungiyoyin tsattsauran ra’ayi.
Ya kuma ce dalilin da ya sa Nijeriya ke magana kan rikicin Gaza, harin da aka kai Qatar da sauran tashin hankula a yankin shi ne saboda ƙwarewar da ƙasar ta samu daga irin wannan rikice-rikice da ba sa ƙarewa inda aka fara.
Shugaban ya ƙara da cewa Nijeriya tana goyon baya ga shirin babban sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya na UN80 Initiative, wanda ya yi kira da a sauya tsarin hukumar domin ya dace da zamani, a kuma kawo ƙarshen maimaita ayyuka da ɓata kuɗi.
No comments