Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Yadda Aka Kama Mai Yi Wa 'Yan Ta'adda Jigilar Miyagun Ƙwayoyi

Jami'an Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa, NDLEA sun samu nasarar kama wani mai suna Baba Kaka Ibrahim ɗan kimanin sh...

Jami'an Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa, NDLEA sun samu nasarar kama wani mai suna Baba Kaka Ibrahim ɗan kimanin shekaru 26 a lokacin da ya ke ɗauke da wasu miyagun ƙwayoyi a motar Marsandi ƙirar GLK mai lamba JRE 987 AE a ƙauyen Njimtilo, a ƙoƙarin sa na kai wa 'yan ta'addan Boko Haram da suka addabi jihohin Borno da Yobe.
 
Bayan da jami'an suka tare motar ne, suna bincika sai suka gano ya cusa waɗannan miyagun ƙwayoyi a bangaren injin motar, inda aka samu tramadol 39,380 da exol-5, duk ya saƙa su a sassan injin.

Hukumar ta yi zargin cewa wannan mutum da ake zargi ya jima yana yi wa 'yan ta'addan safarar miyagun ƙwayoyin a jihohin Yobe da Borno, inda kuma na'urar ma'aikatan Hukumar ta NDLEA ta gano cewa akwai ƙwayoyin a motar.
 

No comments