Matatar Mai da iskar gas ta Ɗangote ta bayyana matakin yajin aikin ƙungiyar ma'aikatan kamfanonin man fetur da iskar ta ƙasa, PENGASSAN ...

A ranar Litinin ne ƙungiyar ƙungiyar ta PENGASSAN ta shiga yajin aiki na sai baba ta gani saboda matakin matatar Ɗangoten na korar wasu ma'aikatan ta kimanin 800.
Ita kuma matatar, a cikin wata sanarwa da ta fitar, ta bayyana cewa, ta sallami ma'aikatan ne a wani mataki na ƙoƙarin daidaita tsarin aikin matatar.
Bangarorin biyu sun tashi baran-baran a wata tattaunawar da suka yi ƙarƙashin jagorancin Ministan ƙwadago na Njeriya, Mohammed Dingyadi a ranar Litinin.
Wannan yajin aiki na PENGASSAN ya shafi rufe ɓangarori da dama na harkar mai a Nijeriya, ciki kuwa har da babban kamfanin mai na ƙasa, NNPCL, tare da dakatar da ba matatar Ɗangote ɗanyen mai.
Kungiyar ta PENGASSAN ta ja daga, inda ta bayyana cewa, "Muna kan bakar mu har yanzu, saboda mutanen mu da aka kora daga aiki, muna so dole a mayar da su."
Wannan na zuwa ne a yayin da wata kotu Abuja ta bayar da umarnin hana yajin aikin ƙungiyar ta PENGASSAN da ɗaukar matakin hana kai wa matatar Ɗangote ɗanyen mai da iskar gas.
Matatar Ɗangote ce ta shigar da ƙarar a gaban kotun ma'aikata a Abuja, kuma Alƙalin kotun ya ce Matatar Ɗangote kamfani ne mai zaman kansa da ke da lasisin samarwa da raba man fetur domin buƙatun 'yan Nijeriya.
Sai ga shi kuma duk da umarnin kotun, ƙungiyar ƙwadago ta NLC a Nijeriya ta yi barazanar shiga yajin aikin domin nuna goyon baya ga PENGASSAN.
No comments