Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

PENGASSAN Ta Janye Yajin Aiki

Ƙungiyar Manyan Ma'aikatan Man Fetur da Iskar Gas ta Nijeriya (PENGASSAN) ta amince da jingine yajin aikin da shiga bayan samun sabani d...



Ƙungiyar Manyan Ma'aikatan Man Fetur da Iskar Gas ta Nijeriya (PENGASSAN) ta amince da jingine yajin aikin da shiga bayan samun sabani da matatar mai ta Dangote

Yajin aikin ne zuwa ne bayan PENGASSAN ta zargi mattaar da korar fiye da ma'aikata 800 saboda sun nuna sha'awar shiga ƙungiyar.

Gwamnatin Nijeriya ce ta shiga tsakani a sasancin ɓangarorin biyu da ake yi tun ranar Litinin, to amma sai a yau Laraba ne aka cimma matsaya.

Cikin wata sanarwa da ma'aikatar kwadagon ƙasar ta fitar ta ce matatar ta amince da mayar da ma'aikatan da ta kora domin su ci gaba da aiki da ita.

"Babu ma'aikacin da zai cutu sakamakon saɓanin matatar Dangote da PENGASSAN," a cewar sanarwar.

A nata ɓangare, ƙungiyar ta PENGASSAN ta ''amince ta fara shirye-shiryen janye yajin aikin''.

Tun bayan fara aikin matatar Dangote a 2024 ta riƙa cin karo da rassan ƙungiyoyin ƙwadago a fannin man fetur na ƙasar, wadanda ke zarginta da ƙoƙarin mamaye harkokin kasuwancin man fetur a ƙasar.

To sai dai matatar ta zargi wasu kamfanonin mai na duniya ne da ke aiki a Najeriya, da ingiza ƙungiyoyin ƙwadagon domin cimma muradunsu.

No comments