Daga Ibrahim Muhammad, Kano An yi bikin buɗe katafaren rukunin shagunan zamani na 'Tropical mall' da kamfanin MC Dream Concept ya g...
Daga Ibrahim Muhammad, Kano
An yi bikin buɗe katafaren rukunin shagunan zamani na 'Tropical mall' da kamfanin MC Dream Concept ya gina a harabar filin tsohuwar Otel ɗin "Royal tropicana da ke Kano.
Bikin buɗe shugaban na "Tropicana mall "da aka gudanar a safiyar ranar talata ya sami halartar 'yan kasuwa da dama, waɗanda suka yi fatan alhairi da yabawa ga waɗanda suka samar da kasuwar.
Kwamishinan kasuwanci na jihar kano, Gwani Shehu Wada Gagagi, ɗaya daga manyan baƙi a taron, a yayin jawabin sa ya nuna damuwa akan yadda 'yan kasuwa masu kanfanoni ba sa jajircewa wajen ɗorewar masana'antun su
Ya yi nuni da cewa a wasu wurare, Kanfanoni ana kafa su shekaru masu yawa suna ayyuka, sun wanzu tun daga kakanni da iyaye, da jikoki, sun shafe shekaru masu yawa ba tare da tsayawa ba.
Daga nan cei Sagagi ya ce suna shirin kiran taro na yin bita da zai ƙunshi 'yan kasuwa da masu kamfanoni don tattauna yadda za a sami kafa masana'antu da yadda za su ɗore ana tafiyar da su ba tare da gazawa ba.
Kwamishinan ya yi fatan alheri da gina shagunan na "Tropicana mall," inda ya ce kuma gwamnatin jihar za ta ci gaba da bayar da goyon baya da zai bunƙasa kasuwanci a jihar Kano.
Da yake zantawa da 'yan jarida, shugaban kamfanin "MC Dream concept" da suka gina shugaban "Tropicana mall," Injiniya Dakta Isma'ila Zubair ya bayyana matuƙar jin daɗin sa bisa kammala ginin cikin nasara, har aka zo ranar da ake ƙaddamarwa.
Ya yi nuni da cewa ba ƙaramin abu ba ne ka zo ka sa abu a gaba, Allah ya taimaka ka fara ka gama lafiya, babu wata matsala, babu wanda ya yi rauni a yayin aikin ginin, ko aka sami wani abu mara daɗi, sun gode wa Allah .
Injiniya dakta Isma'il Zubair ya ce ginin na "Tropicana mall "da aka buɗe yana da shaguna 624 da manyan shaguna "mall" guda biyu da wajen sayar da abinci, da Banki da masallaci da kuma 'yan tebura na ƙananan 'yan kasuwa.
Ya ce tun soma ginin sun bi ƙa'idodi na samun amincewar Gwamnati har suka kammala aikin, sun sami goyon bayan gwamnati
Shugaban kamfanin ya ce, an soma aikin ginin ne a watan Janairu 2022, aka buɗe aka gama 30 ga Satumba 2025, wanda tun fari an tsara kammala ginin ne a cikin watanni 18, amma saboda yanayin yadda aka sami kai a ƙasar nan na hauhawar farashin kaya da ya shafi kayan gini, sai aka sami tsaiko har sai wannan lokaci.
Daga ya yi kira ga jama'a da suke da tsofaffin wurare da ba su san yadda za su yi ginu a zamanance ba, to su tuntube su a ofisoshin su na Kano ko Abuja ko na Lakoja, za su zo su duba su ga yadda za su haɗa kai a ga abin da za a yi da zai bunƙasa ci gaban kasuwanci a wurin.
No comments