Gwamnatin Tarayya ta Nalijeriya ta ƙaddamar da dabarun sadarwa da sababbin tsare-tsare na shekaru uku domin wayar da kan al’umma kan manufof...
Gwamnatin Tarayya ta Nalijeriya ta ƙaddamar da dabarun sadarwa da sababbin tsare-tsare na shekaru uku domin wayar da kan al’umma kan manufofin ilimi da ɗorewa akan su.
An gabatar da shirin ne a birnin Abuja ta hannun Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, inda Ministan Ilimi, Dr Maruf Tunji Alausa, ya ce dabarun za su tabbatar da cewa sauye-sauyen ilimi a ƙarƙashin shirin Renewed Hope na Shugaba Bola Ahmed Tinubu suna isa ga jama’a cikin sauƙi da fahimta.
Ya bayyana wasu daga cikin nasarorin da aka samu, ciki har da:
• Ƙarfafa fannin fasaha da koyon sana’o’i (TVET), inda ɗalibai sama da 960,000 suka yi rajista, kuma an tura fiye da 58,000 zuwa cibiyoyin koyarwa.
• Fara ba da kyauta ta makarantu, masauki da tallafin kuɗi ga ɗaliban kwalejojin fasaha daga shekarar karatun 2025/2026.
• Gina ajujuwa 4,900 na karatu, gyara guda 3,000, da kuma samar da kujeru da tebura 353,000, wanda da ya amfani ɗalibai sama da Miliyan 2.3.
• Mayar da yara sama da 35,000 da suka dena zuwa makaranta don ci gaba da neman ilimi.
Ministan ya kuma bayyana cewa uwargidar shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta tara fiye da Naira Biliyan 21 domin aikin babban ɗakin karatu na kasa.
A nata jawabin, Ƙaramar Ministar Ilimi, Farfesa Suwaiba Sa’id Ahmad, ta ce an tsara shirin tare da goyon bayan PLANE da Hukumar Ci gaban Kasashen Duniya ta Birtaniya (UK International Development) domin karfafa hulɗa da al’umma da samun sahihan ra’ayoyi.
No comments