Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

YIWUWAR AMBALIYAR RUWA: Gwamnatin Kaduna Ta Ƙaddamar Da Shirin Ko-ta-Kwana, Ta Gargaɗi Al’umma

Gwamnatin Jihar Kaduna ta buƙaci ɗaukacin al’ummar jihar da su kasance cikin shirin ko-ta-kwan sakamakon hasashen da Hukumar Hasashen Yanayi...


Gwamnatin Jihar Kaduna ta buƙaci ɗaukacin al’ummar jihar da su kasance cikin shirin ko-ta-kwan sakamakon hasashen da Hukumar Hasashen Yanayi ta Ƙasa (NiMet) da Hukumar Kula da Hanyoyin Ruwa ta Ƙasa (NIHSA) suka bayar, inda suka nuna yiyuwar samun guguwar iska da ruwan sama mai yawa a faɗin jihar daga ranar Laraba, 10 zuwa Litinin, 15 ga Satumba, 2025.

A wata Sanarwar manema labarai da Hukumar bayarnda agajin gaggawa ta Jihar Kaduna (KADSEMA) ta fitar, ta jaddada hatsarin da hakan zai iya haifarwa, kamar ambaliya, cika titi da ruwa a cikin birane, ƙaruwa a matakin koguna, da kuma yiwuwar asarar dukiya, amfanin gona da ababen more rayuwa..

A saboda haka ne Kwamishinan yaɗa labaran jihar  Kaduna, Malam Ahmed Maiyaki ya bayyana cewa gwamnati ta sanya dukkan hukumomin da suka dace cikin shirin ko-ta-kwana domin kare rayuka da dukiyar jama’a.

Ya ce, “Gwamnatin Jihar Kaduna ta shirya tsaf domin ɗaukar matakin gaggawa kan kowanne yanayi da ka iya tasowa sakamakon wannan hasashen yanayi.

"An umurci KADSEMA da ta yi aiki tare da dukkan hukumomi masu ruwa da tsaki domin tabbatar da cikakken shiri. Ana roƙon jama’a da su bi dukkan umarnin kariya, su share magudanan ruwa, kuma su guji wuraren da ambaliya ke yawan faruwa a wannan lokaci."

Hakazalika, Sakataren Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Kaduna (KADSEMA), Dakta Usman Hayatu Mazadu, ya jaddada muhimmancin kasancewa cikin shiri da kuma bin matakan kariya da ke cikin sanarwar.

“Hasashen yanayi ya nuna cewa za a samu guguwar iska da ruwan sama mai yawa musamman a ranakun Laraba da Alhamis. Muna roƙon jama’a da su guji fita ba dole ba yayin ruwan sama mai ƙarfi, su daina ƙoƙarin tuƙi cikin hanyoyin da ruwa ya mamaye, sannan su nisantar da yara daga guraren da ruwa ke taruwa. Manoma kuma su gaggauta ɗaukar matakan kare amfanin gona da wuraren ajiya,” in ji Dakta Mazadu.

“Mun tura tawagar gaggawa  zuwa shiyyoyi daban-daban, kuma ana ƙarfafa gwiwar jama’a da su rika hanzarta bayar da rahoton duk wani lamari na ambaliya ko wata gaggawa da ke barazana ga rayuka ta hanyar amfani da layukan gaggawa na hukuma na KADSEMA,” in ji shi.

Gwamnatin ta kuma yi kira ga jama’a da su kasance cikin natsuwa amma a kasance cikin shiri, tana mai jaddada bukatar haɗin kan al’umma wajen rage haɗurran da ke tattare da yanayin da ake sa ran zai faru.
 

No comments