Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamna Dauda Lawal, Masu Iƙirarin Iyayen Gidan Jihar Zamfara Da Batun Takaicin Da Ke Haifar Da Ƙeta

 Daga Sulaiman Bala Idris Ku yi hasashen shekarar da muke, babu laifi a yin haka. A wannan shekarar da aka haife ni, wani masani ya tashi (t...


 Daga Sulaiman Bala Idris

Ku yi hasashen shekarar da muke, babu laifi a yin haka. A wannan shekarar da aka haife ni, wani masani ya tashi (tare da ƙarfafa 'redeveloped'), wanda ya yi bayani akan ra'ayin takaicin da ke haifar da ƙeta, ma'ana 'Frustration-aggression'. Wataƙila wannan yana ɗaya daga cikin dalilan da nake jin alaƙa ta musamman da batun tun ina karatun digiri na.

Hasashen takaicin da ke haifar da ƙeta ra'ayi ne a Kimiyyar Zamantakewa wanda masana halayyar ɗan adam kamar John Dollard, Neal Miller, Leonard Doob, Orval Mowrer, da Robert Sears suka samar a littafinsu mai suna ‘Frustration and Agression a 1939. Neal Miller ya faɗaɗa akan ra'ayin a cikin 1941, kuma Leonard Berkowitz ya ci gaba da bunƙasa batun a 1939.

Waɗannan masana sun ce, idan abin takaici ya sameka alhali kana daf da cimma burinka, ya fi ban haushi da harzuƙawa, wanda shi ya fi komai jefa mutum ga aikata ƙeta.

A ƙa'ida, duk lokacin da mutane suka yi takaici, su kan mayar da martani mai tsanani. Idan ba za su iya mayar da martani ga wanda ya bata musu rai kai tsaye ba, su kan juya fushinsu zuwa wani abu ko wani wanda ba shi da alaƙa da su baki ɗaya.

Shin dole ne na sake gaya muku dalilin da ya sa wasu 'yan siyasa a Zamfara ke ihun banza da labaran ƙarya? Mu ƙulla alaƙa a tsakanin waɗanda ake kira masu zaman kansu na Zamfara da batun saka fushi a inda bai dace ba. Me ya sa suke takaici? Mene ne kuma wa ya bata musu rai? Yaushe takaici ya shige su?

Wannan takaici dai ya faro ne tun a watan Maris ɗin shekarar 2023, lokacin da gari ya waye, jami’in zaben INEC ya yi wani jawabin da ya shiga tarihi cewa, Lawal Dauda na jam’iyyar PDP, bayan ya cika sharuɗɗan doka, an bayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara, kuma aka rantsar da shi a matsayin zababben gwamnan Zamfara.

Dauda Lawal, sabon zababben gwamna, ya zama abin takaici ga masu iƙirarin iyayen gidan Zamfara ne su, wanda ya kai ga matakan ƙeta. Ba za su iya bata sunan Gwamna Lawal kai tsaye ba saboda tabo kamar su. Bai taba riƙe muƙamin gwamnati ba. Ya fito daga kamfanoni masu zaman kansu.

Waɗannan masu takaicin da ake kira ’yan iyayen gidan Zamfara sun karkatar da fushinsu ne ta hanyar lalata duk wani abu da ke da alaƙa da Jihar Zamfara (abin kunya). Hakan ya haifar da yin kamfen na batanci da yaɗa labaran ƙarya domin kawo cikas ga sauye-sauyen da ake yi a ƙarƙashin Kwamandan Ceto, Dauda Lawal na runduna 377,726.

Ba sabon abu ba ne; Zan iya kiran shi sabon al'ada ga masu yi wa jihar bita-ta-ƙulli (kamar masu takaici da ake kira iyayen gidan Zamfara) da kuma sha'awar ƙirƙirar wani abu a kusa da sunan Dauda Lawal.

Zan maimaita, duk abin da ke kewaye da Dauda Lawal labari ne da ya kai ya yaɗa. Yana jan hankalin mutanen da ba su da rayuwar da suke buƙata. Ga wasu, musamman waɗanda ake kira iyayen gida a jihar Zamfara, iskar shaƙa ce; dole suna buƙatar ta don rayuwa tsira.

Tambayi talakawan Nijeriya daga Legas zuwa Yola, Maiduguri zuwa Abakaliki, game da Dauda Lawal, ​​Gwamnan Zamfara. Za ku ji labari daban-daban da yabo iri-iri. Wasu suna kiransa da hamshaƙin attajirin gwamna. A dandalin Instagram da kafofin watsa labarun Gen Z, shi ne saurayin da suka ƙi yarda ya kai shekaru 60. ’Yan jarida suna kiransa da murya, marar tsoro, kuma haziƙin Dauda.

Abu mafi muhimmanci, shi ne na al’ummar Zamfara. A wajensu Dauda kwamanda ne mai kula da aikin ceto wanda ya mayar da halin da ma’aikata ke ciki na bacin rai ya zama rayuwa ta mutunci da 'yanci. Shi ne mutumin da ya mayar da asibitocin jihar cikin hayyacin su. Shi ne mutumin da ya farfaɗo da ilimi ta hanyar canja munanan labarin jihar na zama a ƙarshe baya a matakin ilimin ƙasa.

A tarihin jihar ba a taba samun gwamna mai kishin ma’aikata kamar Dauda ba. A cikin shekaru biyu kacal da ya yi yana mulki, ya fitar da zunzurutun kuɗi har Naira Biliyan 13.6 a kuɗaɗen biya bashin albashi wanda gwamnatocin baya suka ƙi biya tun 2011 da gangan.

Ga talakawan Zamfara, Dauda shi ne mutumin da ya gyara dukkan manyan asibitoci 14 na Zamfara. Haka kuma, dukkansu an sa musu na’urori na zamani, wanda tsohon shugaban ƙasa Obasanjo ya shaida a lokacin da yake ƙaddamar da asibitin ƙwararru na Yariman Bakura. Ya ce, “Na san wasu asibitocin koyarwa da ba su da na'urar CT scan da MRI, wasu suna da injina, amma ba sa aiki, a nan Zamfara kuna da su kuma suna aiki ga al'umma.

Dauda yana yin abubuwan al'ajabi a Zamfara. A duk lokacin da wani ɗan takaici da ake kira mai gidan Zamfara ya yi haushi, a nuna masa bidiyon filin jirgin sama da ya kammala da kashi 70 wanda ke shirin fara aiki. Wannan mutumin bai zo don wasa ba. Shi ba ɗan siyasa kamar kowa ba ne. Ba iya saka sutura kawai ba ne, akwai kwakwalwa da sanin makamar aiki.

Tasirin Dauda Lawal ya mamaye ƙananan hukumomi 14 na Zamfara, inda ake gudanar da ayyukan raya ƙasa da dama da suka haɗa da makarantu, cibiyoyin kiwon lafiya, da cibiyoyin koyar da sana’o’i. Gwamnatinsa na inganta ababen more rayuwa da ayyukan jin daɗin jama'a, kuma gine-ginen tituna yana inganta haɗin kai ga mazauna.

Don Allah, me ya sa waɗannan da ake cewa masu gida da suka yi ritaya ba za su ji takaici ba? Dauda zai ci gaba da ba su takaici. Zamfara na inganta.

Sulaiman, shi ne Kakakin Gwamnan jihar Zamfara.

No comments