Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bayar da umarnin a gaggauta sakin lamunin Naira Biliyan 250 ga ƙananan manoma a faɗin Nijeriya...

Umarnin, wanda aka bai wa Hukumar Kula da Samar da Abinci ta Fadar Shugaban Ƙasa (PFSCU), na zuwa ne da nufin hanzarta rabon bashin wanda shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da shi don bunƙasa noman rani a yayin da ake tsaka da damuna don tabbatar da ci gaba da samar da wadataccen abinci ba tare da ƙaƙƙautawa ba.
Mataimakin Shugaban ƙasar ya gargaɗi hukumar da cewa dole ta gaggauta samar da tsarin aiwatar da rabon lamunin ta inda kuɗaɗen za su kai ga manoman da abin ya shafa ba tare da jan ƙafa ba, inda ya ce gwamnati ba za ta lamunci gafara-sa ba ta ga ƙaho ba.
A cewar sa " Gwamnatin Shugaba Tinubu ta samar da shirin ne don ganin 'yan Nijeriya sun amfana akan lokaci ba don ajiyar kuɗaɗe ba"
Shettima, wanda ya yaba wa irin gudumawar da Shugaba Tinubu, ya bai wa hukumar PFSCU dama don yin gyaran-fuska ga tsare-tsaren samar da abinci ba tare da tarnaƙi ba, musamman a bangaren sassauta hanyoyin samar da kayan haɗa taki da kafa asusun tallafin Shugaban Kasa.
Ya ƙara da cewa "Idan ma'aikatun Gwamnatin Tarayya, hukumomi da masana'antu masu zaman kansu za su haɗa kai, ƙudirin gwamnati zai samar da ayyukan ci gaban ƙasa na zahiri cikin ƙanƙanin lokaci,"
Tuni dai gwamnoni da masu ruwa da tsaki da suka sami halartar taron suka yaba da wannan matsayar da gwamnatin ta ɗauka,
inda suka ce za su bayar da duk wani goyon baya ga kwamitin shugaban ƙasar don ganin an samar da tsari mai kyau wajen rabon tallafin
No comments