Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Matasa 573,523 Ne Suka Nemi Aikin Gurabe 3,927 Da Za A Ɗauka A Kwastam

Hukumar hana fasa ƙwabri ta ƙasa 'Nigeria Customs Service (NCS)' ta bayyana cewa sakamakon sanarwar da ta wallafa a wasu jaridun ƙas...


Hukumar hana fasa ƙwabri ta ƙasa 'Nigeria Customs Service (NCS)' ta bayyana cewa sakamakon sanarwar da ta wallafa a wasu jaridun ƙasar nan ranar 27 ga watan Disambar da ya gabata, na shirin ɗaukar ma'aikata, yanzu haka mutum 573,523 ne suka rubuto takardar neman aiki, a gurabe 3,927 za ta ɗauka.

Shugaban sashen wayar kai da hulɗa da jama'a na Hukumar, ACC Abdullahi Maiwada ne ya bayyana haka a wata sanarwar ƙarin haske da ya sanya wa hannu, inda ya bayyana irin shirye-shiryen da hukumar ke yi na ɗaukar sabbin ma'aikatan a matakai daban-daban.

Ya ce, bayan da aka tantance waɗancan takardun neman aiki, an zabo mutum 286,697 waɗanda suka cancanci zuwa matakin tantancewa na gaba, wanda za a yi a tsakanin kwanakin 14 ga Satumba zuwa 21 Satumbar nan. Shi ma zai gudana ne ta internet, wato 'Computer-Based Test (CBT).' "Wannan na nuni da irin gaskiya da gaskiya da aka shirya don ɗaukar cancanta," in ji Hukukar.

Sanarwar ta ƙara da cewa, waɗanda suka samu nasarar shiga jerin sunayen da aka ware, to, za su yi gwaji a inda suka ga ya fi masu kusa, matuƙar akwai wadatacciyar intetnet a wurin. " Wajibi ne ya zama mutum yana da kwamfuta babba ko ƙarama, mai abin ɗaukar hoto (webcam), domin wayoyin hannu ba za su yi ba," in ji sanarwar.

Haka kuma ana buƙatar mutum ya zama ya yi shiga mai kyau, saboda a kauce wa samun wata matsala wajen ɗaukar hoto, domin a gane mutum da kyau.

Hukumar ta ce, za a rinƙa sanar da matakin tantancewa na gaba ga duk waɗanda suka cancanta, ta hanyar sadarwa da Hukumar ta tanada na ƙashin kanta. 

 

No comments