Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Masanin Harkar Tsaro, Bulama Bukarti, Ya Ƙaryata Iƙirarin El-Rufai Kan Biyan ’Yan Bindiga Kuɗaɗen Fansa

 Wani masanin tsaro, Dr. Bulama Bukarti, ya ƙaryata iƙirarin da tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya yi cewa gwamnatin tarayya ta...


 Wani masanin tsaro, Dr. Bulama Bukarti, ya ƙaryata iƙirarin da tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya yi cewa gwamnatin tarayya tana biyan kuɗaɗen fansa tare da samar da kayayyaki ga ’yan bindiga da ke addabar Nijeriya.

El-Rufai ya yi wannan zargi ne a shirin Sunday Politics na tashar Channels TV, inda ya dora alhakin tabarbarewar tsaro a kan gwamnati.

Sai dai a martanin sa, Dr. Bukarti ya ce kalaman El-Rufai ba su da tushe, yana mai bayyana su da cewa “siyasa ce tsagwaronta babu gaskiya.” Ya bayyana cewa babu wata doka ko manufa da ta bai wa gwamnati damar biyan ’yan bindiga ko kuma tallafa musu. 

A cewar sa, kuɗaɗen fansa da ake yawan ji ana biya, yawanci iyalan waɗanda abin ya shafa ko al’ummar su ne ke tarawa.

Ya kuma bayyana cewa rahotanni sun nuna ’yan bindiga sun karɓi sama da Naira Biliyan 2.5 a shekarar 2025 kaɗai, adadin da ya ce babu wata gwamnati da za ta iya ɗauka.

Masanin tsaron ya ce matsalar tsaro a Nijeriya ta fi ƙarfin dabarun soja kaɗai, inda ya danganta ta da cin hanci da rashawa wanda ya kira “babban mai ba da damar ayyukan ta’addanci.” 

Ya yi gargaɗin cewa ya zama dole a guji yin zarge-zargen da ba su da tushe kan shugabannin da ke kan karagar mulki, yana mai tunatar da cewa irin wadannan maganganu an taba yi a kan gwamnatocin baya ma.

Yayin da yake bayani kan tsarin rundunar sojoji. Bukarti ya jaddada cewa shugaban ƙasa ne kaɗai ke da ikon bayar da umarnin ɗaukar matakin soja.
Ya ce gwamnoni, ministocin tsaro da ma mai ba da shawara kan harkokin tsaro ba su da wannan iko. 

A cewar sa, tsarin umarni daga shugaban ƙasa yake farawa zuwa Babban Hafsan Soja, sannan daga can zuwa kwamandojin filin daga.

A ƙarshe, Dr. Bukarti ya ce magance matsalolin tsaro a Najeriya na bukatar dogon lokaci, hadin gwiwa tsakanin gwamnati, hukumomin tsaro da ’yan kasa, tare da tsaurara matakan yaki da cin hanci da rashawa.

No comments