Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Sama Da ‘Yan Nijeriya Miliyan 20 Ne Suke Amfana Da Tsarin Inshorar Lafiya -NHIS

 Hukumar Kula da Inshorar Lafiya ta Ƙasa (NHIS) ta bayyana cewa sama da ‘yan Nijeriya Miliyan 20 ne suka shiga tsarin inshorar lafiya a faɗi...


 Hukumar Kula da Inshorar Lafiya ta Ƙasa (NHIS) ta bayyana cewa sama da ‘yan Nijeriya Miliyan 20 ne suka shiga tsarin inshorar lafiya a faɗin ƙasar nan.

Muƙaddashin Shugaban Kwamitin Yankin Arewa ta Tsakiya wanda ya haɗa jihohin Kwara, Neja da Kogi, Alhaji Adamu Abdullahi ne yabayyana hakan a wata hira da ya yi da kamfanin dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) a Ilorin cikin makon dabya gabata.

Alhaji Adamu ya ce ana gudanar da wannan shiri ne domin wayar da kan jama’a game da manufofin hukumar wajen samar da ingantaccen tsarin kiwon lafiya, tare da cimma burin Universal Health Coverage (UHC) nan da 2030.

Ya bayyana cewa Nijeriya na sa ran samun mutane mlMiliyan 44 a tsarin, domin sauƙaƙa samun ingantaccen kiwon lafiya ga ‘yan ƙasa.

Ita ma, Hajiya Idayat Bello-Olaitan, Kwamishinan hukjmar ta jihar Kwara, ta ce an fara wasu shirye-shiryen tallafi na musamman, ciki har da shirin CEMONC na gaggauta ceto rayukan mata da jarirai, da shirin Free Fistula da kuma shirin rigakafin cutar HIV/AIDs da Tarin Fuka daga Global Fund.

Ta ƙara da cewa, hukumar za ta fara gudanar da shirin “Mystery Shopping”, don tabbatar da cewa masu inshora ba sa samun matsala wajen samun lafiya a asibitoci, tare da tabbatar da inganci a duk cibiyoyin lafiya.

No comments