Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya umarci kwamitin majalisar zartarwa ta ƙasa (FEC) da ya gaggauta ɗaukar matakan da za su saukar da farashin abi...

Ƙaramin Ministan Noma da Tsaron Abinci, Sanata Aliyu Sabi Abdullahi ne ya bayyana hakan a Abuja ranar Laraba, inda ya ce shugaba Tinubu ya bayar da umarnin tabbatar da cewa ana samun sauƙin jigilar amfanin gona daga gonaki zuwa kasuwanni ba tare da tsadar sufuri ba.
A cewarsa, shugaban ƙasar yana son a samar da tsarin da zai tabbatar da samun abinci mai araha, mai inganci, kuma mai wadatar gina jiki ga ’yan Najeriya, ba kawai samun wadataccen abinci ba.
Ministan ya ce gwamnati za ta ƙaddamar da shirin Farmer Soil Health Scheme don inganta amfanin gona, da kuma sabunta tsarin haɗin kan manoma domin samar da kudade da karfafa gwiwar manoma a karkara.
Ya ƙara da cewa Shugaba Tinubu yana da babban buri a fannin haɗin kan manoma a matsayin wata hanya ta bunƙasa tattalin arziki da inganta rayuwar jama’a.
Tun a watan Yuni, Shugaba Tinubu ya bayyana cewa Najeriya tana kan hanya wajen cimma burin ’yancin samar da abinci a ƙasar, inda ya jaddada bukatar kasar ta dogara da kanta wajen samar da abincin da za ta ci.
No comments