Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya jinjina wa Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, bisa kafawa, tare da jagorantar Majalisar Ƙw...

Da yake jawabi a taron karo na bakwai na Majalisar Ƙasa kan Kwarewa (NCS) a ranar Talata a Fadar Shugaban Ƙasa, Abuja, Mataimakin Shugaban Ƙasa ya ce juyin juya halin ƙwarewa shi ne ginshiƙin yarjejeniyar gwamnatin Tinubu da ‘yan Nijeriya, kuma muhimmin mataki ne wajen cika alƙawarin bunƙasa jari-hujjar ɗan adam.
Ya yaba da misalin da Jihar Kaduna ta bayar, yana mai jaddada cewa jagorancin Gwamna Uba Sani da kuma shigar fiye da dalibai 30,000 cikin Cibiyar Horar da Sana’o’i da Kwarewa ta Kaduna na nuna sahihin ƙudurin samar da ayyukan yi da bunƙasa kwarewar matasa.
Haka zalika, Ministan Ilimi, Dakta Olatunji Alausa , shi ma ya jinjinawa rawar da Gwamna Sani ya taka wajen sauƙaƙa bikin kaddamar da Cibiyar Horar da Sana’o’i da Kwarewa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gudanar, yana mai cewa yanzu haka ana sake fasalin makarantun fasaha na ƙasa baki ɗaya domin su mai da hankali kacokan kan darussa masu amfani da tasiri.
Shettima ya buƙaci mambobin NCS da su haɗa kai bayan wani tsari guda na juyin-juya halin Nijeriya, yana mai gargaɗin cewa "ba za mu iya gina ma'aikata da za su yi shiri a nan gaba kan tushen rarraba."
No comments