Daga Ibrahim Muhammad, Kano Al'ummar musulmi a Nijeriya sun buƙaci mahukunta su saki jagoran al'ummar Falasɗinawa mazauna ƙasar nan,...
Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Al'ummar musulmi a Nijeriya sun buƙaci mahukunta su saki jagoran al'ummar Falasɗinawa mazauna ƙasar nan, Ransy Abu Ibrahim da aka kama aka tsare ba tare da ya aikata wani laifi ba.
Da yake magana da 'yan jarida a jihar Kwara, ɗaya daga cikin al'ummar musulmin, shugaban ƙungiyar Harakatul Islamiyya, Malam AbdulRazak Abdulwahab Al-Ameen ya ce jagoran Falasɗinawan yana zaune a ƙasar nan sama da shekaru 30 ba a taba samun sa da wani abu na karya doka ba .
Ƙungiyoyin suna zargi Isra'ila da hannu a sawa hukumomin ƙasar nan su kama jagoran Falasɗinawan da har yanzu hukumomi ba su bayar da wani bayani kan dalilin kama shin ba.
Ya ce Falasɗinawa a kasar nan shekara da shekaru na zaune lafiya da al'umma don haka take hakkin su ne kama jagoransu da bai aikata wani laifi ba.
Kungiyoyin addinin musulunci sun ja hankalin Gwamnatin ƙasar nan cewa ta saki shugaban Palasdiwan.
No comments