Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Yadda Ɗan Nijeriya Ya Yi Kutse A Amurka Ya Wawure $235,266 Ta Intanet

Hukumar shari’a ta Amurka ta bayyana cewa an cafke wani ɗan Nijeriya mai suna Farouk Adekunle Adepoju, wanda ke zaune a Birtaniya. An kama m...



Hukumar shari’a ta Amurka ta bayyana cewa an cafke wani ɗan Nijeriya mai suna Farouk Adekunle Adepoju, wanda ke zaune a Birtaniya.

An kama matashin ne bisa zargin kutse ta kwamfutoci da damfara da ta kai ga asarar $235,266 (Sama da Naira miliyan 300).

An kama shi a ranar 15 ga Satumba, 2025, inda hukumomin Birtaniya suka fara shirye-shiryen mika shi ga Amurka domin fuskantar shari’a a Pennsylvania.

Rahoton tuhumar ya nuna cewa tsakanin watan Maris zuwa Afrilu 2023, Adepoju ya kutsa cikin kwamfutar wani kamfanin gine-gine da ke aiki tare da jami’a a Pennsylvania.

Bayan kutsen, an ce ya sauya imel din kamfanin, ya ƙirƙiri asusun imel na bogi, sannan ya yaudari jami’ar ta aika kuɗi zuwa wani asusu na jabu.

Lauyan Amurka, Troy Rivetti, ya bayyana cewa Adepoju ya yi amfani da dabaru na zamani wajen shiga asusun wani kamfani da kuma karkatar da kuɗi daga jami’ar.

Troy Rivetti ya ce, hakan babban laifi ne da ya yi barazana ga tsaro da dukiyar jama’a.

Rivetti ya ƙara da cewa, “Kodayake yana can a wani yanki na duniya, hakan bai hana FBI gano shi da kuma ɗaukar matakin kawo shi gaban shari’a ba.”

Shugaban ofishin FBI na Pittsburgh, Kevin Rojek, ya ce wannan lamari darasi ne ga duk masu laifi da ke tunanin za su iya yin kutse daga nesa domin tara dukiya.

Ya jaddada cewa FBI ba za ta lamunci irin waɗannan ayyuka ba, kuma tana da haɗin gwiwa da sauran hukumomi wajen kamo masu aikata laifi ko da suna waje.

Rahoton ya tabbatar da cewa Adepoju na fuskantar tuhuma bakwai, ciki har da shida na damfarar waya, wanda kowanne zai iya jawo hukuncin shekaru 20 a kurkuku idan aka same shi da laifi.

Haka kuma akwai tuhuma guda ɗaya ta kutse a kwamfuta, wacce take ɗauke da hukuncin shekaru biyar a gidan yari.

A cewar rahoton, har yanzu ba a samu kuɗin da aka karkatar ba, wanda hakan ya kara ɗaga girman laifin da ake tuhumarsa da shi.

A halin yanzu, Adepoju yana tsare a hannun hukumomin tsaron Birtaniya yayin da ake jiran cikar takardun shari’ar mika shi zuwa Amurka. 

No comments